To ni kada kasanyayi sheda tunda haka ne; don ni bana shaidar Zur

To ni kada kasanyayi sheda tunda haka ne; don ni bana shaidar Zur

Daga Nu'aman Dan Bashir ya ce: Babana yayi mun kyautar wani abu daga cikin kudinsa, sai Mahaifiyata Amrah 'Yar Rawahata ce: Ba an taba yarda ba har sai Annabi ya shaida sai Mahaifina ya tafi wajen Annabi don ya kafa shaida da kyautar da yayi mani, sai Annabi yace da shi ko kayi irin wannan kayutar ga sauran 'yayanka? sai yace AA sai ya ce: " kuji tsoron Allah kuma kuyi Adalci gaY'ayan ku, sai Mahaifina ya dawo, kuma ya fasa wannan kyautar" a cikin lafazin wata riwayar kuwa: "To ni kada kasanyayi sheda tunda haka ne; don ni bana shaida kan Zalunci" a cikin wani lafazin kuma: "Nemi shaidar wani ba ni ba"

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim Suka Rawaito shida Riwayoyin nasa daban daban]

الشرح

Nu'aman Dan Bashir ya gaya Mana cewa Mahaifinsa ya bashi wata kyauta ta Musamman daga cikin Dukiyarsa sai Mahaifiyarsa ta so ta tabbatar da shaidar kyautar sai ta nemi Mahaifin sa yaje ya kafa shaida a wajan Annabi akanta, yayin da Mahaifin ya je wajen Annabi don ya yi masa Shaida, sai ya ce da shi: ko kayi irin wannan kyautar ga sauran 'Ya'yanka baki daya? Sai ya ce: AA kuma kebance wasu yaran abar wasu ko fifita wasunsu wannan aikin yana kore tsoron Allah kuma shi cewa Zalunci ne sabida Barnar da ke cikinsa, domin yana Sabbaba gaba da kiyayyarsu ga yan uwansu da aka fifitasabida kasancewar wadan nan abubuwan barnar Annabi ya ce: da shi "kaji tsoron Allah kuma ka daidaita tsakanin 'yayanka kuma kada ka sani Shaida akan abinda yake Zalunci ne" kuma ya yi Masa fada kuma ya haneshi ga barin aikatawa da fadinsa: ka nemi shaidar wani ba ni ba dai, to daga babu abinda ya ke kan Bashir sai ya fasa wannan kyautar kamar yadda akasan Sahabbai da tsayawa cik idan akazo kan hakkin Allah.

التصنيفات

Ciyarw da 'Ya'ya