Lallai Allah ba Ya karɓar aiki sai wanda ya zama abin tsarkakewa, kuma aka nufi fuskar Allah da shi

Lallai Allah ba Ya karɓar aiki sai wanda ya zama abin tsarkakewa, kuma aka nufi fuskar Allah da shi

Daga Abu Umama al-Bahili - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum ya zo gurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Shin kana ganin mutum ya yi yaƙi yana neman lada da yabo, me gare shi? sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ba shi da komai". Sai ya maimaita masa sau uku, tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana ce masa: "Ba shi da komai" sannan ya ce: "Lallai Allah ba Ya karɓar aiki sai wanda ya zama abin tsarkakewa, kuma aka nufi fuskar Allah da shi".

[Ingantacce ne] [Al-Nasa'i Ya Rawaito shi]

الشرح

Wani mutum ya zo gurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: dan ya tambaye shi ya nemi fatawarsa game da hukuncin mutumin da yake fita yaƙi yana neman lada daga Allah da kuma kwaɗayin yabo da godiyar mutane, shin zai samu lada? sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bashi amsa: Da cewa bashi da komai na lada; dan abinda ya yi wa Allah tarayya da shi a cikin niyyarsa, sai mutumin ya maimaita tambayarsa sau uku ga Annabi - tsira da amincin Allaah su tabbata agare shi -, kuma tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana amsa masa wannan amsar; da cewa bashi da lada, sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bashi labarin cewa ka'idar karbar aiki a wurin Allah: Lallai cewa Allah ba Ya karbar aiki sai in ya zama dukkansa saboda Allah ne batare da tarayya da wani a cikinsa ba, kuma ya zama dan zatin Allah ne - tsarki ya tabbatar maSa -.

فوائد الحديث

Allah ba Ya karɓar ayyuka sai abinda ya zama tsarkakakke ga Allah - Maɗaukakin sarki -, da kuma dacewar shiriyarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agagtre shi -.

Yana daga kyanwun amsa fatawar mai bada fatawa fatawarsa ta zama ta cika manufar mai tambaya da ma ƙari.

Karfafa al'amari mai girma ta hanyar maimaita tambaya game da shi.

Mai yaƙi na gaskiya shi ne wanda ya yi yaƙi dan kalmar Allah ta zama maɗaukakiya, da kuma neman lada da sakamako na lahira tare da tsarkake niyya, badan yaƙinsa ya zama dan duniya ba.

التصنيفات

Falalar Ayyukan Zukata