إعدادات العرض
Ku saurara, lallai kowannenku yana ganawa ne da Ubangijinsa, dan haka kada sashinku ya cutar da sashi
Ku saurara, lallai kowannenku yana ganawa ne da Ubangijinsa, dan haka kada sashinku ya cutar da sashi
Daga Abu Sa'id al-Kudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi i'itikafi a cikin Masallaci, sai ya ji su suna bayyanar da karatu, sai ya yaye mayafi, sai ya ce: «Ku saurara, lallai kowannenku yana ganawa ne da Ubangijinsa, dan haka kada sashinku ya cutar da sashi, kada kuma sashinku ya ɗaga muryarsa ga sashi a cikin karatu», ko cewa ya yi: «A cikin sallah».
[Ingantacce ne] [Abu Daud Ya Rawaito shi]
الترجمة
العربية Português دری Македонски Tiếng Việt Magyar ქართული Bahasa Indonesia বাংলা Kurdî ไทย অসমীয়া Nederlandsالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana zaune yana i'itikafi a cikin wata ƙubba a cikin Masallacinsa dan neman kusanci ga Allah, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ji sahabbansa suna bayyanar da karatun Alƙur'ani a bayyane mai tsanani sashinsu yana cutar da sashi. Sai ya yaye mayafi daga ƙubbar, ya zargi wanda ya aikata haka ya zarge shi, sai ya ce: Dukkaninku kuna ganawa ne da Ubangijinku ta hanyar karatun Alƙur'ani, dan haka kada sashinku ya cutar da sashi, kuma kada sashinku ya ɗaga muryarsa akan sashi a cikin karatu, ko a cikin sallah.فوائد الحديث
Hani akan ɗaga murya a karatun Alƙur'ani, idan ya kasance a akwai cutarwa ga wani a cikinsa.
Koyarwar da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga sahabbansa ladubann karartun Alƙur'ani.
التصنيفات
Ladaban Karatun Al-qur'ani