Na rantse da wanda raina yake hannunSa, lallai cewa ita ta yi daidai da ɗaya bisa uku na Alƙur'ani

Na rantse da wanda raina yake hannunSa, lallai cewa ita ta yi daidai da ɗaya bisa uku na Alƙur'ani

Daga Abu Sa'id al-Kudri - Allah Ya yarda da shi -: Cewa wani mutum ya ji wani mutum yana karanta: {Ka ce Shi ne Allah Shi kaɗai}, yana maimaita ta, lokacin da ya wayi gari sai ya zo wurin manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya fada masa hakan, kai ka ce mutumin yana ganin ƙanƙantarta, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Na rantse da wanda raina yake hannunSa, lallai cewa ita ta yi daidai da ɗaya bisa uku na Alƙur'ani".

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

Abu Sa'id al-Khudr - Allah Ya yarda da shi - ya fadi cewa wani mutum ya ji wani mutumin daban yana karanta Suratu (Ikhlas): {Ka ce Shi ne Allah Shi kaɗai} yana maimaitata a kowanne dare ba ya ƙari akanta, lokacin da ya wayi gari sai ya zo gurin manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ambata masa haka, kamar shi mai maganar yana ganin cewa ta yi kaɗan, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi rantsuwa akan ma'anar ƙarfafawa: Na rantse da wanda raina yake a hannunSa lallai cewa ita (Surar) ta yi daidai da ɗaya bisa uku na Alƙur'ani.

فوائد الحديث

Falalar Suratul Ikhlas, kuma ita tana daidai da ɗaya bisa uku na Alƙur'ani.

Halaccin karatu a sallar tsayuwar dare koda da ayoyi kaɗan ne da kuma maimaita su, da rashin ƙaranta hakan.

AlMaziri ya ce: An ce: Ma'anarsa: Cewa Alƙur'ani yana da ɓangarori uku; Kissoshi da hukunce-hukunce da kuma siffofin Allah - Maɗaukakin sarki -, {Ka ce Shi ne Allah Makaɗaici} mai tacewa ce - yana nufin ga siffofin Allah -, dan haka ita ce ɗaya bisa uku, kuma wani yanki daga cikin yankuna uku. Kum an ce: Ma'narsa: Cewa ladan karantata ana ninka shi da gwargwadan ladan karatun ɗaya bisa uku na Alƙur'ani ba tare da ninkawa ba.

التصنيفات

Falalar Surori da Ayoyi