{Shin yanzu kwa mayar da shayar da mai aikin Hajj da kuma raya Masallaci mai alfarma kamar wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira}[al-Taubah: 19] karanta ayar har zuwa ƙarshenta

{Shin yanzu kwa mayar da shayar da mai aikin Hajj da kuma raya Masallaci mai alfarma kamar wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira}[al-Taubah: 19] karanta ayar har zuwa ƙarshenta

Daga Nu'umanu Ibnu Bashir - Allah Ya yarda da su - ya ce: Na kasanace a wurin minbarin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai wani mutum ya ce: Bayan na musulunta babu ruwana da in yi wani aiki sai dai kawai in shayar da mai yin aikin Hajji. Wani kuma ya ce: Bayan na musulunta babu ruwana da in yi wani aiki sai dai in raya Masallaci mai alfarma. Wani kuma ya ce: Jihadi a tafarkin Allah ya fi abin da kuka faɗa, sai Umar ya yi musu tsawa, kuma ya ce: Kada ku ɗaga muryarku a wajen mimbarin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali ranar Juma'a ce, sai dai idan na sallaci Juma'a zan shiga in tambaye shi a cikin abin da kuka saɓa a cikinsa, sai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya saukar da: {Shin yanzu kwa mayar da shayar da mai aikin Hajj da kuma raya Masallaci mai alfarma kamar wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira}[al-Taubah: 19] karanta ayar har zuwa ƙarshenta.

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Nu'umanu Ibnu Bashir - Allah Ya yarda da su - ya ambaci cewa shi yana zaune a wajen mimbarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ji wani mutum yana cewa: Bayan na musulunta ba zan damu dana aikata wani aiki ba sai dai in shayar da mai aikin Hajji. Wani kuma ya ce: Bayan na musulunta ba zan damu dana aikata wani aiki ba sai dai in raya Masallaci mai alfarma. Wani kuma ya ce: Jihadi a tafarkin Allah ya fi abin da kuka faɗa. Sai Umar Ibnul Khaɗɗabi - Allah Ya yarda da shi- ya yi musu tsawa saboda ɗaga muryarsu da suka yi a wajen mimbarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma safiyar ranar Juma'a ce, sai dai idan na yi sallar Juma'a zan shiga in tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a kan abin da kuka saɓa a cikinsa, sai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya saukar da: {Shin, kun mayar da shãyar da mahajjata da rãyar da Masallaci Mai alfarma kamar wanda ya yi ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira, kuma ya yi jihãɗi a cikin hanyar Allah? Bã su daidaita a wurin Allah. Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai} [al-Tauba: 19].

فوائد الحديث

Fifikon ayyuka a lada da sakamako.

Fifikon ayyuka gwargwadan abin da shari'a ta zo da shi, bawai gwargwadan ƙoƙarin mutane ba.

Falalar Jihadi a tafarkin Allah da sharaɗin yin imani da Allah ne da kuma ranar lahira.

Nawawi ya ce: A cikinsa akwai karahiyar ɗaga murya a cikin masallatai a ranar Juma'a da waninta, kuma mutum kada ya ɗaga murya da ilimi ne ko da waninsa a lokacin taruwar mutane dan yin sallah saboda abin da ke cikinsa na takura musu da kuma masu yin sallar da kuma masu yin zikiri.

التصنيفات

Dalilan Saukar Ayoyi, Hukunce Hukuncen Huxubar Jumu'a