إعدادات العرض
Ku barta lallai ita (ɗabi'a ce) mai wari
Ku barta lallai ita (ɗabi'a ce) mai wari
Daga Jabir Ibnu Abdullah -Allah Ya yarda da su - ya ce: Mun kasance a cikin wani yaƙi, sai wani mutum daga cikin Muhajirun ya daki bayan wani mutum daga cikin mutanen Madina, sai mutumin Madina ya ce: Yaku mutanen Madina ku kawo mini agaji, wanda ya yi hijira kuma ya ce: Yaku muhajirai ku kawo mini agaji, sai Allah Ya jiyar da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: «Mene ne wannan?» sai suka ce: Wani mutum ne daga Muhajirun ya daki bayan wani mutum daga cikin mutanen Madina, sai mutumin Madinan ya ce: Yaku mutanen Madina ku kawo mini agaji, wanda ya yi hijira kuma ya ce: Yaku Muhajirun kukawo mini agaji, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Ku barta lallai ita (ɗabi'a ce) mai wari ». Jabir ya ce: Mutanen Madina sun kasance a lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo Madina sun fi yawa, sannan Muhajirun suka yi yawa bayan nan, sai Abdullahi Ibnu Ubay ya ce: Shin sun aikata kuwa, wallahi idan muka koma Madina sai maɗaukaka sun fitar da maƙasƙanta, sai Umar Ibnul Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ya Manzon Allah ka barni in daki wuyan wannan munafikin, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «ka bar shi, kada mutane suce lallai (Annabi) yana kashe sahabbansa».
الترجمة
العربية Português دری Македонски Magyar Tiếng Việt ქართული Kurdî বাংলা ไทย অসমীয়া Nederlands ਪੰਜਾਬੀ Bahasa Indonesia Kiswahiliالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana halin tafiya a wani yaƙi a tare da shi akwai sahabbansa Muhajirun da kuma Ansarawa - Allah Ya yarda da su -, sai wani mutum daga Muhajirun ya daki bayan wani mutum daga Muhajirun da hannunsa. Sai mutumin Madinan ya ce: Ku taimakeni yaku Ansarawa, wanda kuma ya yi hijira ya ce: Ku taimakeni yaku Muhajirun, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ji sai ya ce: Mene ne wannan? Sai suka ce: Wani mutum ne daga Muhajirai ya daki bayan wani mutum cikin Ansarawa da hannunsa, sai mutumin Madinan ya ce: Ku kawo mini agaji yaku Ansar, wanda ya yi hijira kuma ya ce: Ku kawo min agaji yaku Muhajirun. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ku bar wannan al'adar ta Jahiliyya domin ita mummuna ce abar ƙyama mai cutarwa; ita ce cewa mutum idan abokin rigimarsa ya rinjaye shi sai ya kira mutanensa sai su yi gaggawar taimakonsa alhali shi ne ya kasance azzalimin ko kuma shi ne wanda aka zalinta dan jahilci dake garesu da kuma ƙabilanci. Jabir ya ce: Ansarawa sun kasance lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo Madina yana mai hijira sune mafi yawa, sannan bayan nan Muhajirun suka yi yawa. Sai shugaban munafukai Abdullahi Ibnu Ubayy ibnu Salul ya ce: Al'amarin yakai wannan haddin?! Wallahi idan muka koma Madina sai masu rinjaye - wato yana nufin shi da waɗanda ke tare da shi - sun fitar da ƙasƙantattu - wato yana nufin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da waɗanda ke tare da shi daga Madina. Umar Ibnul Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ya Manzon Allah ƙyaleni in daki wuyan wannan munafukin, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: ƙyale shi, dan kada mutane su dinga cewa Muhammad yana kashe mabiyansa ko da azahiri ne.فوائد الحديث
Hani daga al'adaun Jahiliyya ababen zargi da kuma irin ɗabi'unsu, a magana ko aikatawa, Musulunci ya zo ne dan nisantar da mutane daga hakan, da kuma shiryar da su zuwa abin da yake shi ne daidai da kuma gaskiya garesu.
Gargaɗarwa daga yin ƙungiyancin ƙarya da kuma tsoratarwa daga abin ƙyama mara kyau.
Hani daga dukkanin abin da yake haifar da gaba da kuma ƙiyayya.
Nawawi ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci hakan da da'awa irin ta Jahiliyya ne dan yaƙi hakan ne, domin hakan ya kasance akan abin da Jahiliyya suke a kansa ne na neman ɗauki da ƙabilu a cikin al'amuran duniya da abubuwan da ke rataye da su, a Jahiliyya sun kasance suna ɗaukar fansarsu da ta'assubanci da kuma ƙabilu, sai Musulunci ya zo ya ɓata hakan, ya rarrabe bayanai da hukunce-hukunce na shari'a, idan wani mutum ya yi ta'addanci akan wani sai alƙali ya yi hukunci a tsakkaninsu, ya kuma lazimta masa abin da zalincinsa ya hukunta kamar yadda ya tabbata daga ƙa'idojin Musulunci.
Sindi ya ce: Sai ya bayyana cewa nasara dan kasancewar sa ne daga ƙabilarsa kamar yadda ma'abota Jahiliyya suke akai to ɓatacce ne. Dan haka babu wata fuska akan kowane mutum ya kira ƙabilarsa, amma taimakon gaskiya to abin nema ne kuma lazimi ne akan kowane mumini daidai ne ya kasance daga ƙabilarsa ne ko kuma a'a.
Abin da munafukai suke a kansa na magana mara kyau da kuma yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da sahabbansa - Allah Ya yarda da su - ƙarfin hali.
Abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake a kansa na tsananin juriya da kuma haƙuri akan abin da yake samunsa na cutarwar munafukai.
Gargaɗarwa akan dukkanin aikin da a cikinsa akwai kore mutane daga shiga cikin Addinin Musulunci, saboda haka ne Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana a kashe munafukai dan kada mutane su dinga cewa: Lallai (Annabi) Muhammad yana kashe sahabbansa.
التصنيفات
Munanan Halaye