إعدادات العرض
Lallai a cikin aljanna akwai wata kasuwar da 'yan aljanna suke zuwanta kowacce Jumu'a
Lallai a cikin aljanna akwai wata kasuwar da 'yan aljanna suke zuwanta kowacce Jumu'a
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai a cikin aljanna akwai wata kasuwar da 'yan aljanna suke zuwanta kowacce Jumu'a, sai iskar arewa ta taso sai ta watsu a fuskokinsu da tufafinsu, sai su ƙara kyau da ƙawa. sai su koma zuwa ga iyalansu alhali haƙiƙa sun ƙara kyau da ado, sai iyalansu suce musu: Wallahi haƙiƙa kun ƙara kyau da ƙawa a bayanmu, sai su ce: Kuma wallahi haƙiƙa kun ƙara kyau da ado a bayanmu".
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Tiếng Việt සිංහල Kurdî Nederlands Kiswahili অসমীয়া ગુજરાતી Magyar ქართული Românăالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa a cikin aljanna akwai wani wurin da zasu dinga taruwa a wurin, babu siye da siyarwa a cikinsa suna ɗaukar abinda suke so daga gare shi, suna zuwa wurin gwargwdan kwana bakwai, sai iskar arewa ta taso, sai ta motsa a fuskokinsu da tufafinsu, sai su ƙara kyau da ƙawa, sai su koma zuwa ga iyalansu alhali haƙiƙa sun ƙara kyau da ƙawa, sai iyalansu su ce musu: Wallahi haƙiƙa a bayanmu kun ƙara kyau da ƙawa, sai su ce: Kuma wallahi haƙiƙa kun ƙara kyau da ƙawa a bayanmu.فوائد الحديث
Bayanin cewa 'yan aljanna suna samun ƙaruwar kyau da ƙawa.
Hadisan suna sawa mutum kwaɗayi a cikin aiki nagari wanda ake taka shi zuwa wannan gidan.
An keɓanci iskar arewa da ambato ne; domin cewa ita ta kasance mafi kyan iska a wurin larabawa yayin da take zuwa da alheri da kuma ruwa.
Kwaɗaitarwa akan kira zuwa ga Allah ta hanyar kwaɗaitar da aljanna da kuma ni'imarta.
التصنيفات
Sifar Al-janna da Wuta