«‌Lallai Allah Yana azabtar da waɗanda suke azabtar da mutane a duniya».

«‌Lallai Allah Yana azabtar da waɗanda suke azabtar da mutane a duniya».

Daga Hisham Ibnu Hakim Ibnu Hizam - Allah Ya yarda da su - cewa shi ya wuce wasu mutane daga cikin manoma a Sham, haƙiƙa an tsaida su a cikin rana, sai ya ce: Meke damunsu? suka ce: Antsaresu ne saboda jizya, sai Hisham ya ce: Na shaida cewa na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: «‌Lallai Allah Yana azabtar da waɗanda suke azabtar da mutane a duniya».

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Hisham Ibnu Hakim Ibnu Hizam - Allah Ya yarda da su - ya wuce wasu manoma daga baubayi a Sham, an tsayar da su a zafin rana, sai ya yi tambaya game da lamarinsu? Sai aka ba shi labarin cewa su an aikata musu haka ne saboda basu bada (jizya ba) alhali su suna da ikon hakan. Sai Hisham - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ina shaida cewa na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: Lallai Allah Yana azabtar da waɗanda suke azabtar da mutane a duniya akan zalinci ba tare da wani haƙƙi ba.

فوائد الحديث

Jizya ita ce: Dukiyar da aka wajabtawa maza daga cikin ma'abota littafi (Yahudawa da Nasara) baligai mawadata maimakon kiyayesu da kuma zamansu a kasar Musulunci.

Haramcin azabtar da mutane har kafirai ba tare da wani abinda yake wajabta hakan na shari'a ba.

Gargaɗar da azzalumai daga zalinci.

Riƙon sahabban Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da horo da aikin alheri da kuma hani daga abin ƙi.

Nawawi ya ce: Wannan abin ɗauka ne akan azabtarwa ba tare da wani haƙƙi ba, dan haka azabtarwa da haƙƙi bata shiga cikinsa kamar ƙisasi, da haddi, da ta'azirai, da makanacin haka.

التصنيفات

Munanan Halaye