Kada ɗayanku ya kuskura ya yi sallah da tufa ɗaya, babu komai a kafaɗunsa

Kada ɗayanku ya kuskura ya yi sallah da tufa ɗaya, babu komai a kafaɗunsa

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Kada ɗayanku ya kuskura ya yi sallah da tufa ɗaya, babu komai a kafaɗunsa".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana wanda ya yi sallah a tufa ɗaya ya tsiraitar da kafaɗunsa abinda ke tsakanin kafaɗa da wuya ta inda kada, ya sarayar da wani abinda zai suturtasu; domin kafaɗu biyu duk da ba al'aura ba ne, to lallai suturtasu ya fi tabbata a ɓoye al'aura, kuma shi ne mafi kusanci zuwa girmama Allah - Maɗaukakin sarki - da girmamaShi a tsakiyar tsayuwa a gabanSa a cikin sallah.

فوائد الحديث

Halaccin sallah a tufa ɗaya idan ya suturta abinda suturta shi yake zama wajibi.

Halaccin sallah a tufa biyu, ɗayansu zai suturta saman jiki, ɗayan kuma zai suturta ƙasansa.

An so kasancewar mai sallah (ya kasance) a kyakkyawar siffa.

Wajabcin suturce kafaɗu biyu ko ɗayansu a cikin sallah, idan hakan ya tabbata gare shi , an ce hanin na tsarkaka ne (bana haramci ba ne).

Karancin abinda ke a hannun sahabbai - Allah Ya yarda da su - na dukiya, har sashinsu ba ya mallakar tufa biyu.

AlNawawi ya ce a ma'anar hadisin: Hikimarsa cewa shi idan ya ɗaura shi alhali bai kasance akwai wani abu akan kafaɗarsa ba ba'a amintuwa cewa al'aurarsa ta yaye, saɓanin idan ya sanya sashinsa akan kafaɗarsa, kuma domin shi zai iya buƙatuwa zuwa ya kamo shi da hannunsa ko da hannayensa sai ya shagalta da hakan, sai sunnar ɗora hannun dama akan na hagu ƙarƙashin ƙirji da kuma ɗaga su inda aka shara'anta ɗaga su dama wanin hakan su wuce shi; domin a cikinsa akwai barin suturce saman jiki da wurin ado, alhali haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Ku riƙi adonku a kowane masallaci} [al-Aaraf: 31].

التصنيفات

Saraxan Sallah