«‌Alƙiyama ba zata tashi ba har sai mutane sun dinga yin alfari da massalatai».

«‌Alƙiyama ba zata tashi ba har sai mutane sun dinga yin alfari da massalatai».

Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «‌Alƙiyama ba zata tashi ba har sai mutane sun dinga yin alfari da massalatai».

[Ingantacce ne]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa: Yana daga cikin alamomin kusancin ranar alƙiyama da kuma ƙarewar duniya mutane zasu dinga alfahari da ƙawata masallatansu, ko kuma alfaharinsu da duniyarsu a cikin masallatan da ba'a ginasu ba sai dan ambatan Allah.

فوائد الحديث

Haramcin yin alfahari da masallatai, kuma hakan aiki ne ba karɓaɓɓe ba; domin ba'a aikata shi saboda Allah ba.

Hani daga ƙawata masallatai da kaloli, da kuma fenti kala-kala da kuma zane-zane, da rubce-rubuce; dan abinda ke cikinsu na shagaltar da masallata a yayin kallonsu.

Sindi ya ce: Wannan hadisin yana daga abinda duniya ta yi masa shaida, kuma hakan yana daga cikin jumlar mu'ujizoji bayyanannu gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

التصنيفات

Hukunce Hukuncen Masallaci