Wanda ya tsarkake Allah a bayan kowacce sallah sau talatin da uku, kuma ya gode wa Allah sau talatin da uku, ya yi wa Allah Kabbara sau talatin da uku, wancan (lissafin) shi ne casa'in da tara kenan, kuma yace a cikon ɗarin: (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai Yake ba Shi da abokin…

Wanda ya tsarkake Allah a bayan kowacce sallah sau talatin da uku, kuma ya gode wa Allah sau talatin da uku, ya yi wa Allah Kabbara sau talatin da uku, wancan (lissafin) shi ne casa'in da tara kenan, kuma yace a cikon ɗarin: (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai Yake ba Shi da abokin tarayya, mulki ya tabbata gareShi, godiya ta tabbata gareShi, kuma Shi mai iko ne a kan dukkan komai), za'a gafarta masa kurakuran sa, ko da sun kasance tamkar kumfar kogi

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya tsarkake Allah a bayan kowacce sallah sau talatin da uku, kuma ya gode wa Allah sau talatin da uku, ya yi wa Allah Kabbara sau talatin da uku, wancan (lissafin) shi ne casa'in da tara kenan, kuma yace a cikon ɗarin: (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai Yake ba Shi da abokin tarayya, mulki ya tabbata gareShi, godiya ta tabbata gareShi, kuma Shi mai iko ne a kan dukkan komai), za'a gafarta masa kurakuran sa, ko da sun kasance tamkar kumfar kogi".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya ce bayan ƙare sallar farilla: Sau talatin da uku: "Tsarki ya tabbata ga Allah" (Subhanallah) shi ne tsarkake Allah daga tawaya. Da kuma talatin da uku: "Godiya ta tabbata ga Allah" (Alhamdulillah) shi ne yabo gareShi da siffofin cika tare da sonSa da girmamaShi. Da talatin da uku: "Allah ne Mafi girma" (Allahu Akbar) shi ne cewa Allah ne Mafi girma kuma Mafi ɗaukaka daga dukkan komai. Da cike adadin ɗarin da faɗin: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai yake, ba shi da abonkin tarayya, kuma Shi mai iko ne a kan dukkan komai. Ma’anarsa: Babu abin bauta da cancanta sai Allah Shi kaɗai, ba shi da abonkin tarayya, kuma Shi Maɗaukakin Ya keɓanta da cikakken mulki, wanda ya cancanta da Yabo da kambamawa tare da so da girmamawa banda wanda ba shi ba, kuma Shi mai iko ne babu abin da yake gagarar sa. Wanda ya faɗi hakan an shafe masa kurakuransa kuma an gafarta masa su, ko da sun kasance kwatankwacin farar kunfa ce wacce take saman kogi lokacin da ya kwaranyo.

فوائد الحديث

An so yin wannan zikirin bayan sallolin farilla.

Wannan zikirin sababi ne na gafarar zunubai.

Girman falalar Allah - Maɗaukakin sarki - da rahamarSa da gafararSa.

Wannan zikirin sababi ne na gafarar zunubai, abin nufi: Kankare ƙananan zunubai, amma manyan zunuban babu abinda yake kankaresu sai tuba.

التصنيفات

Zikirin Sallah