Ana yanke hannu a rubu'un dinari (ɗaya bisa huɗu) zuwa sama

Ana yanke hannu a rubu'un dinari (ɗaya bisa huɗu) zuwa sama

Daga Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Ana yanke hannu a rubu'un dinari (ɗaya bisa huɗu) zuwa sama".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa ɓarawo ana yanke hannunsa saboda satar rubu'in dinari na zinare, da abinda ya ƙaru a kan hakan, kuma ya yi daidai da abinda ƙimarsa ta yi daidai da ƙimar 1.06 Gram na zinari.

فوائد الحديث

Sata tana daga cikin manyan zunubai.

Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - Ya iyakance uƙubar ɓarawo, ita ce yanke hannunsa; kamar yadda yake a cikin faɗinSa - Maɗaukakin sarki -: {Barawo da ɓarauniya to ku yanke hannayensu} [al-Ma'ida: 38], kuma sunnah ta bayyana sharuɗɗan wannan yankewar.

Abin nufi da hannu a cikin hadisin shi ne yanke tafi daga gaɓarsa tsakaninsa da tsakanin damtse.

Daga hikima a cikin yanke hannun ɓarawo, (akwai) kiyaye dukiyoyin mutane, da tsawatar da waninsa (ɓarawon) cikin masu ta'addanci.

Dinari awo ne na zinare, kuma ya yi daidai a yanzu da (4.25 KG) awon 24; to ɗaya bisa huɗu na dinari ya yi daidai da Gram da wani abu.

التصنيفات

Haddin Sata