Bawa na ya rigaye ni da kansa, don haka a haramta masa Aljanna

Bawa na ya rigaye ni da kansa, don haka a haramta masa Aljanna

Daga Jundubu Dan Abdullahi Albujali -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "An yi wani mutum cikin wadanda suka gabace ku yana da wani ciwo sai ya yanke kauna, ya dauki wuka ya yanke hannunsa, jini bai dauke ba har ya mutu. Sai Allah yace: Bawa na ya rigaye ni da kansa, don haka Na haramta masa Aljanna".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi tsira da amincin Allah ya bawa sahabbansa labarin wani utum cikin al'ummar da suka gabace mu ya kasance yana da wani rauni mai azabar ciwo, sai ya karaya ya yanke kauna da warkewa, ya kasa yin hakuri da azabar da yake sha, ko dan neman lada ma a wajen Allah, saboda karancin imani da sakankancewa da Allah, sai ya dauki wuka ya yanke hannnun da ita, sai jini ya yi ta zuba, yaki tsayawa har mutumin ya mutu. Sai Allah yace: Maanar abin da yace: Wannan bawa na ne ya kagara ga zuwan rahama ta da waraka ta, ba shi da dauriya kan jarabawa ta, saiya yi gaggawar hallaka kansa, yayi tsammanin ya rage ajalinsa ta hanyar kashe kansa, sai Na haramta masa shiga Aljanna,, wanda aka haramtawa Aljanna kuwa, to wuta ce makomarsa.

التصنيفات

Zargin Savo