Ya Allah ina neman tsari da yardarKa daga fushinKa, da kuma rangwaminKa daga uƙubarKa, kuma ina neman tsari da Kai daga gareKa ba zan iya ƙididdige yabo gareKa ba kamar yadda Ka yabi kanKa

Ya Allah ina neman tsari da yardarKa daga fushinKa, da kuma rangwaminKa daga uƙubarKa, kuma ina neman tsari da Kai daga gareKa ba zan iya ƙididdige yabo gareKa ba kamar yadda Ka yabi kanKa

Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na rasa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wani dare a shinfiɗa sai na lalube shi sai hannuna ya faɗa akan cikin diga-digansa alhali shi yana cikin masallaci alhali su suna a kafe, alhali shi yana cewa: "Ya Allah ina neman tsari da yardarKa daga fushinKa, da kuma rangwaminKa daga uƙubarKa, kuma ina neman tsari da Kai daga gareKa ba zan iya ƙididdige yabo gareKa ba kamar yadda Ka yabi kanKa".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na kasance ina barci a gefen Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai na rasashi da daddare, sai na laluba da hannayena gurin da ya kasance yake sallah a cikinsa a cikin ɗaki; sai gashi yana sujjada alhali diga-digansa suna a tsaye, sai gashi shi yana cewa: (Ina neman tsari) ina kamun ƙafa (da yardarKa daga fushinKa) akaina ko akan al'ummata, (kuma) ina neman tsari (da rangwaminKa) afuwarKa mai yawa (daga uƙubarKa), (Ina neman tsari daga gareKa) da siffofin kyawunKa daga siffofin ɗaukakarKa, inda ba mai fakewa daga gare Ka sai Kai, babu matserata kuma babu mafaka daga Allah sai dai zuwa gareShi, (Ba zan iya ƙididdige yabo a gareKa ba) ba zan iya kuma bazan kai ƙololuwa a lissafewa ba da kuma ƙirgawa ba saboda gajiyawata ba, ƙididdige ni'imarKa da kyautatawarKa kamar yadda Kake cancantarsa ba koda na yi ƙoƙari a hakan. (Kai kamar yadda Ka yabi kanKa) Kaine wanda Ka yi yabo akan zatinKa yabon da ya dace da Kai, waye yake da iko akan bada haƙƙin yabonKa?!

فوائد الحديث

An so waɗannan addu'o'in a cikin sujjada.

Mirak ya ce: A cikin ɗaya daga riwayoyi al-Nasa'i: Ya kasance yana faɗin wannan addu'ar idan ya gama sallarsa ya koma makwancinsa.

An so yabo ga Allah da siffofinSa da kuma roƙonSa da sunayenSa tabbatattu a cikin Littafi da Sunnah.

A cikinsa akwai girmama Mahalicci a cikin ruku'u da sujjada.

Halaccin neman tsari da siffofin Allah, kamar yadda neman tsari da zatinSa - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - yake halatta.

AlKhaɗɗabi ya ce: A cikin wannan maganar akwai ma’ana mai kyau, ita ce: Cewa shi haƙiƙa ya nemi tsarin Allah Ya tsare shi da yardarSa daga fushinSa, da kuma rangwaminSa daga uƙubarSa, yarda da fushi kishiyoyi ne masu fuskantar juna, haka nan rangwami da kamu da uƙuba, lokacin da ya zama zuwa anbatan abinda bask shi da kishiya Shi ne Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - ya nemi tsari da Shi daga gareShi bada waninSa ba, ma'anar haka: Istigfari domin kasawa wurin cika wajibi daga haƙƙin bayinSa, da yabo a gareShi. da faɗinSa: ba zan iya ƙididdige yabo a gareka ba: Wato ba zan iya shi ba, kuma ba zan iya kai matuka a cikinsa ba.

التصنيفات

Zikirin Sallah