Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana ƙoƙari a cikin goman ƙarshe irin ƙoƙarin da ba ya yi a cikin waninsa

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana ƙoƙari a cikin goman ƙarshe irin ƙoƙarin da ba ya yi a cikin waninsa

Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita -: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana ƙoƙari a cikin goman ƙarshe irin ƙoƙarin da ba ya yi a cikin waninsa.

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan goman ƙarshe ya zo na Ramadan yana ƙoƙari a cikinsu da yin ibada da ɗa'a, kuma yana kai matuƙa a cikin nau'ikan alherai da sinfofin ayyukan kirki da ibadu mafi yawa daga abinda yake ƙoƙari a cikin waninsa; hakan dan girma da falalar waɗancan dararen da kuma dan neman daren Lailatul Ƙadr.

فوائد الحديث

Kwaɗaitarwa akan yawaita alheri da fuskokin ayyukan ɗa'a a cikin watan Ramadan a hade da kuma goman ƙarshe daga gare shi a keɓance.

Goman ƙarshe na Ramadan suna farawa ne daga daren ashirin da ɗaya har zuwa ƙarshen wata.

An so ribatar lokuta mafifita da ayyukan ɗa'a.

التصنيفات

Goman Qarshe na Watan Azumi