إعدادات العرض
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan goman ƙarshe ta shiga zai raya dare, zai farkar da iyalansa, zai yi ƙoƙari zai ɗaure gwabso
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan goman ƙarshe ta shiga zai raya dare, zai farkar da iyalansa, zai yi ƙoƙari zai ɗaure gwabso
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan goman ƙarshe ta shiga zai raya dare, zai farkar da iyalansa, zai yi ƙoƙari zai ɗaure gwabso.
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी ئۇيغۇرچە Kurdî Português සිංහල Kiswahili অসমীয়া Tiếng Việt ગુજરાતી Nederlands አማርኛالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan goman ƙarshe na Ramadan ya shiga zai rayar da dukkan dare da nau'ikan ayyukan ɗa'a, kuma ya farkar da iyalansa dan yin sallah, ya yi ƙoƙari a cikin ibada ƙari akan al'adarsa, ya duƙufa gareta, kuma ya nisanci matansa.فوائد الحديث
Kwaɗaitarwa da ribatar mafifitan lokuta da ayyuka na gari.
AlNawawi ya ce: A cikin wannan hadisin: Cewa an so a yi ƙari daga ibadu a cikin goman ƙarshe na Ramadan, kuma an so raya dararensa da ibadu.
Yana kamata ga bawa ya zama mai kwaɗayi akan iyalansa da umartarsu da yin ibada, kuma ya yi haƙuri akansu.
Aikata alherai yana buƙatuwa zuwa ƙudirin niyya da haƙuri da dagewa.
AnNawawi ya ce: Malamai sun yi saɓani a ma'anar (ya ɗaure gwabso) an ce: Shi ne ƙoƙari a cikin ibadu ƙari akan al'adarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a waninsa, kuma ma'anarsa: Zage damtse a cikin ibadu, ana cewa; Na ɗaure gwabso na dan wannan al'amarin, wato: Na zage damtse gare shi na yi ƙoƙari, an ce: Shi kinaya ne game da nisantar iyali dan shagaltuwa da ibadu.
التصنيفات
Goman Qarshe na Watan Azumi