إعدادات العرض
«Ya Allah lallai ni ina neman tsarinKa, daga munanan ɗabi'u da ayyuka da soye-soyen rayuka».
«Ya Allah lallai ni ina neman tsarinKa, daga munanan ɗabi'u da ayyuka da soye-soyen rayuka».
Daga Ƙuɗbah ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cewa: «Ya Allah lallai ni ina neman tsarinKa, daga munanan ɗabi'u da ayyuka da soye-soyen rayuka».
[Ingantacce ne] [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi]
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Kurdî Tiếng Việt Magyar ქართული Kiswahili සිංහල Română অসমীয়া ไทยالشرح
Ya kasance daga cikin addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: (Ya Allah lallai ni ina neman tsari) ina fakewa (da Kai) banda waninKa, (daga munanan) abubuwan da Allah da ManzonSa suka hana su, (ɗabi'u) kamar ƙullata da hassada da girman kai, (da kuma) munanan (ayyuka) kamar zagi, (da) dukkanin (soye-soyen zuciya), waɗanda zuciya take son su alhali sun saɓawa shari'a.فوائد الحديث
Falalar wannan addu'ar kuma an so a yi ta.
Mumini yana kwaɗayi akan nisantar ɗabi'u ababen zargi da kuma munanan ayyuka, kuma yana kiyayewa daga bin son rai da kuma afkawa cikin sha'awowi.
Rarrabuwar ɗabi'u da soye-soyen zuciya zuwa munana da kuma kyawawa.
التصنيفات
Addu’o’I da aka samu daga Annabi