Ya Allah da (kiyayyewar) Ka ne muka wayi gari, kuma da (kiyayewar) Ka ne muka shiga maraice, da (al'amarin) Ka ne muka rayu, kuma da (al'amarin) Ka ne zamu mutu, kuma tashi (daga ƙabari) yana gareKa

Ya Allah da (kiyayyewar) Ka ne muka wayi gari, kuma da (kiyayewar) Ka ne muka shiga maraice, da (al'amarin) Ka ne muka rayu, kuma da (al'amarin) Ka ne zamu mutu, kuma tashi (daga ƙabari) yana gareKa

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - Cewa shi ya kasance idan ya wayi gari yana cewa: "Ya Allah da (kiyayyewar) Ka ne muka wayi gari, kuma da (kiyayewar) Ka ne muka shiga maraice, da (al'amarin) Ka ne muka rayu, kuma da (al'amarin) Ka ne zamu mutu, kuma tashi (daga ƙabari) yana gareKa" Idan ya shiga maraice ya ce: "Da (kiyayewarka) Ka ne muka shiga maraice, kuma da (kiyayewar) Ka ne muka wayi gari, da (al'amarin) Ka zamu mutu, kuma tashi (daga ƙabari) yana gare Ka" ya ce: Wani lokaci kuma: "Makoma tana gare Ka".

[Hasan ne]

الشرح

(Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya kasance idan ya wayi gari shi ne farkon yini tare da ɓullowar alfijir yana cewa: (Ya Allah da (kiyewar) Ka ne muka wayi gari) muna masu cakuɗuwa da kiyayewarKa ababen lulluɓewa da ni'imominKa, masu shagaltuwa da ambatanKa, masu neman taimako da sunanKa, masu tarowa da dacewarKa, masu motsawa da dabararKa da kuma ƙarfinKa, (da (kiyayewar) Ka ne muka shiga maraice, da (kiyayewar) Ka ne muka rayu, da (kiayewar) Ka ne zamu mutu) wato kamar lafazin da ya gabata tare da sanya shi a sama, sai ya ce: Ya Allah da Kai ne muka shiga maraice, kuma da sunanKa ne Mai rayawa muke rayuwa, da sunaKa ne Mai kashewa zamu mutu, (kuma gareKa ne tashi yake) da tashi bayan mutuwa, da rarrabuwa bayan haduwa, halinmu zai ci gaba akan haka a cikin dukkan lokuta, da ragowar halaye ba zan rabu ba daga gare shi kuma ba zan kaurace masa ba. Idan ya shiga maraice bayan la'asar ya ce: "Ya Allah da (kiyayewar) Ka ne muka shiga maraice, kuma da (kiyayewar) Ka ne muka wayi gari, da (umarnin) Ka ne muke rayuwa, kuma (da al'amarin) Ka ne zamu mutu, makoma tana gare Ka) makoma a duniya, da makoma a ƙarshe, Kaine Kake rayani kuma kaine zaKa kasheni.

فوائد الحديث

An so wannan addu'ar safe da yamma, dan koyi da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

Buƙatuwar bawa ga Ubangijinsa a cikin dukkan halayensa da lokutansa.

Abin da yafi a karanta zikirai, a safiya: Daga ɓollowar alfijir zuwa ɓullowar rana a farkon yini, haka kuma daga bayan la'asar zuwa kafin faɗuwar rana, idan ya faɗesu bayan hakan yana nufin: -Ya faɗesu a safiya bayan ɗagawar walaha - ya isar masa, idan ya faɗesu bayan azahar ya isar masa, idan ya faɗesu bayan Magariba ya isar masa, to wannan lokaci ne na zikiri.

Munasabar faɗinsa: " Tashi yana gare Ka" da safe, wannan yana tunatar da shi da rayuwa da tashi babba lokacin da mutane zasu mutu kuma a tashesu ranar alƙiyama, to wannan tashine sabo, kuma yini ne sabo da ake dawo da rayuka a cikinsa, kuma mutane suke watsuwa a cikinsa, wannan sabuwar safiyar wacce Allah Ya halicceta zata nunfasa; dan ta zama mai shaida akan ɗan Adam, kuma lokutansa da sakwankwaninsa su zama taskar ayyukansa.

Munasabar faɗinsa: "Makoma tana gareKa" da yamma, lokacin da mutane suke dawowa daga ayyukansu da watsuwarsu a abubuwan maslahohinsu da rayuwarsu, zasu dawo zuwa gidajensu, zasu dawo zuwa hutu bayan sun rarrabu, sai ya tuna makoma da komawa zuwa ga Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka -

التصنيفات

Zikirin Safiya da Maraice