‌Ya Allah Ka kareni azabarKa ranar da zaKa tara ko zaka tashi bayinKa

‌Ya Allah Ka kareni azabarKa ranar da zaKa tara ko zaka tashi bayinKa

Huzaifa Ibnul Yaman -Allah Ya yarda da shi -: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya yi nufin yin bacci yana sanya hannunsa ƙarƙashin kansa, sannan ya ce: «‌Ya Allah Ka kareni azabarKa ranar da zaKa tara ko zaka tashi bayinKa».

[Ingantacce ne] [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya kwanta dan yayi barci, sai ya shimfiɗa hannunsa na dama kuma ya sanya kundukukinsa (kumatunsa)na dama akansa, sai ya ce: «‌Ya Allah» Ubangijina «‌Ka kareni» Ka kiyayeni daga «‌azabarKa» da uƙubarKa «‌ranar da zaKa tara ko zaKa tashi bayinKa» a ranar hisabi, ranar alƙiyama.

فوائد الحديث

Falalar wannan addu'ar mai albarka, kuma an so kiyayewa a kanta dan yin koyi da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

An so kwanciya akan ɓarin jiki na dama.

Sindi ya ce: Faɗinsa (Ya Allah Ka kareni azabarKa), a cikinsa cewa yana kamata ga mai hankali ya maida baccinsa tsani dan tina mutuwa da kuma tashi a bayanta.

Kariya daga azabar Allah a ranar alƙiyama tana kasancewa ne da falalar Allah da kuma rahamarSa, ta hanyar dacewar bawa ga aiki na gari da kuma gafarar Allah ga bayinSa.

Tawali'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga Ubangijinsa kuma Majiɓincin al'amuransa - Allah Maɗaukakin sarki -.

Tabbatar da taruwa da kuma makoma, kuma cewa mutane masu komawa ne zuwa ga Ubangijinsu dan ya yi musu hisabi akan ayyukansu, wanda ya samu alheri to ya godewa Allah - Maɗaukakin sarki -, wanda ya samu koma bayan haka to kada ya zargi kowa sai kansa, kawai su ne ayyukan bayi Allah Yana kiyaye musu su.

Kwaɗayin sahabbai - Allah Ya yarda da su - akan bayanin halayen Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agagre shi - a baccinsa.

Faɗinsa: "Sai ya sanya hannunsa na dama ƙarƙashin kundukukinsa" ya kasance daga al'adunsa - tsra da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ne damantawa a cikin kowane abu, sai dai abinda dalili ya zo akan saɓaninsa.

Bacci akan ɓarin jiki na dama ya fi saurin farkawa saboda rashin tabbatar zuciya a cikin wannan halin, kuma ya fi sauƙi ga zuciya; domin ita zuciya a ɓangaren hagu take, da a ce bawa ya yi bacci akan ɓarin hagu zai cutar da zuciya dan nauyin gaɓɓai a kanta.

التصنيفات

Ladaban bacci da kuma tashi daga Bacci