Kaffarar bakance ita ce kaffarar rantsuwa

Kaffarar bakance ita ce kaffarar rantsuwa

Daga Uƙubah Ibnu Amir - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Kaffarar bakance ita ce kaffarar rantsuwa».

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa kaffarar bakance kai tsaye idan ba'a iyakance abin da yake nufi daga gareta ba kuma bai ambace shi ba: Ita ce kaffafar rantsuwa.

فوائد الحديث

Bakance: A shari'a shi ne: Mukallafi da zaɓin kansa ya lazimtawa kansa wani abu saboda Allah - Maɗaukakin sarki -.

Kaffarar rantsuwa ita ce: Ciyar da miskinai goma ko a tufatar da su, ko 'yanta wani bawa daga bauta, idan ba zai iya ba to sai azimin kwana uku.

Hikima a kaffara ita ce Musulmi ya girmama bakance dan haka ba zai koma masa ba, kuma ba zai kasance akan harshensa ba.

Na'ukan bakance:

1- Bakance kai tsaye: Kamar faɗinsa: (Na yi alwashi saboda Allah idan na warke) kuma ya yi shiru bai yi niyyar wani ayyanannen alwashin ba, to akansa akwai kaffarar rantsuwa a lokacin da ya warke.

2- Bakance na jayayya da fushi: Shi ne ya rataya bakance da sharaɗi, yana nufin hanuwa daga aikata wani abu ko yunƙurin aikata shi kamar ya ce: (Idan na yi wa wane magana to na wajabtawa kaina azimin wata biyu), hukuncinsa: Shine a ba shi zaɓi tsakanin aikata abin da ya lazimtawa kansa, ko ya yi kaffar rantsuwa idan ya yi masa magana.

3- Bakancen da aka halatta: Misali: (Wallahi na wajabtawa kaina sanya tufafina), hukuncinsa: A bashi zaɓi tsakanin sanya tufafin ko kuma kaffarar rantsuwa.

4- Bakancen da aka karhanta: Misali: (Na ɗorawa kaina abu kaza saboda Allah in ban yi ba zan saki matata), hukuncinsa: An sunnanta masa kaffarar rantsuwa kuma kada ya aikata abin da ya yi bakancen, idan ya aikata shi to babu kaffara a kansa.

5- Bakancen saɓo: Misali (Na yi wa Allah bakancen yin sata) Hukuncinsa: Ya haramta a kansa ya aikata shi kuma wajibi ne ya yi kaffarar rantsuwa, idan ya aikata shi babu laifi kuma babu kaffara a kansa.

6- Bakancen yin aikin ɗa'a misali: (Na yi wa Allah bakancen yin sallah kaza) da nufin neman kusanci zuwa ga Allah, idan ya rataya shi ga wani sharaɗi kamar warakar mara lafiya da shi idan sharaɗin ya tabbata, idan bai rataya shi ba to wajibi ne ya cika shi kai tsaye.

التصنيفات

Rantsuwa da kuma Bakance