Cewa an tambayeta game da karatun Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -

Cewa an tambayeta game da karatun Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -

Daga Ibnu Abi Mulaikah: Daga wata daga cikin matan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - Abu Amir ya ce: Nafi'u Ya ce: Ina zatan Nana Hafsa ce - Cewa an tambayeta game da karatun Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ta ce: Lallai ku ba zaku iya ba, ya ce: Sai aka ce mata bamu labarin yadda karatun yake. Ya ce: Sai ta yi karatun da ta yi a sake, Abu Amir ya ce: Nafi'u ya ce: Sai Ibnu Abi Mulaikah ya hakaito mana {Alhamdu lillahi rabbil Aalamin} [al-Fatiha: 2]. sannan ya yanyanke {Al-rahmanur Rahim} [al-Fatiha: 1] sannan ya yanyanke {Maliki yaumud din}.

[Ingantacce ne] [Ahmad ne ya rawaito shi]

الشرح

An tambayi Nana Hafsa uwar muminai - Allah Ya yarda da ita -: Yaya Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake karanra Alƙur'ani? Sai ta ce: Lallai ku ba zaku iya irin nasa ba, sai aka ce mata; Faɗa mana. Nafi'u ya ce sai Ibnu Abi Mulaikah ya karanta karatun da yayi shi a hankali; dan ta hakaito kuma ta kusanto musu da yadda karatun Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ke, sai ya karanta: {Alhamdu lillhi rabbil Aalamin} sannan ya yanyanke karatun, {Arrahmanur rahim}, sannan ya yanyanke karatun, {Maliki yaumid din}.

فوائد الحديث

Bayanin shiriyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin karatun Alƙur'ani.

Ɗabbaƙawa na ilimi na bayanin kaifiyyar karatun Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

Halaccin yin karatu a hankali kuma hakan ya fi kusanto da Tadabburin ma'anoninsa.

Himmatuwar magabata na gari da Alƙur'ani mai girma da kuma aikin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

Muhimmancin sanin Tajwidi da kuma Ulumul Ƙur'an.

التصنيفات

Ilimin Tajweedi