Wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a matsayinAddini, kuma da Muhammad a matsayin Manzo, Aljanna ta wajaba a gare shi

Wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a matsayinAddini, kuma da Muhammad a matsayin Manzo, Aljanna ta wajaba a gare shi

Daga Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a matsayinAddini, kuma da Muhammad a matsayin Manzo, Aljanna ta wajaba a gare shi».

[Ingantacce ne] [Abu Daud Ya Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya ce: (Na yarda da Allah a matsayin Ubangiji) kuma abin bautawa da gaskiya mai reno kuma mamallaki shugaba kuma mai gyarawa. (Da Musulunci) da dukkanin hukunce-hukuncensa na umarni da hani (Addini) kuma tafarki da shari'a da miƙa wuya. (Da Annabi Muhammad a matsayin manzo) da Annabi; da dukkanin abinda aka aiko shi da shi kuma ya isar da shi garemu, sai aljanna ta wajaba gare shi.

فوائد الحديث

Kwaɗaitarwa a kan faɗar wannan addu'ar, da bayanin ladan da ya jerantu a kanta.

Yarda da Allah a matsayin Ubangiji ta ƙunshi kada mutum ya bautawa waninSa - tsarki ya tabbatar maSa -.

Yarda da (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a matsayin Annabi da Manzo ya ƙunshi yi masa biyayya - aminci ya tabbata agare shi - da jawuwa ga sunnarsa.

Yarda da Musulunci a matsayin Addini shi ne yarda da abinda Allah Ya zaɓe shi ga bayinSa.

An so faɗin wannan addu'ar a yayin shahada biyu daga jin kiran sallah kamar yanda yake a cikin wasu riwayoyin daban.

Kuma ya zo a cikin wani hadisin daban cewa an so wannan addu'ar a safiya da maraice.

التصنيفات

Zikiri da ba su da wani Qaidi