إعدادات العرض
Kada ɗayanku ya yi nuni zuwa ga ɗan uwansa da makami, domin shi bai sani ba wataƙila Shaiɗan ya fizge daga hannunsa sai ya faɗa ciki ramin wuta
Kada ɗayanku ya yi nuni zuwa ga ɗan uwansa da makami, domin shi bai sani ba wataƙila Shaiɗan ya fizge daga hannunsa sai ya faɗa ciki ramin wuta
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Kada ɗayanku ya yi nuni zuwa ga ɗan uwansa da makami, domin shi bai sani ba wataƙila Shaiɗan ya fizge daga hannunsa sai ya faɗa ciki ramin wuta».
الشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi ga musulmi ya nuna ɗan uwansa musulmi da kowane irin makami, domin cewa shi bai sani ba wataƙila Shaiɗan ya ɗauke shi akan motsa makamin a hannunsa, sai ya kashe ɗan uwansa ko ya cutar da shi, sai ya faɗa cikin saɓon da zai kai shi ya faɗa cikin ramin wuta.فوائد الحديث
Bayanin haramcin jinin musulmi.
Wajabcin girmama musulmi da kiyayewa daga sadar da sharri gare shi ta hanyar aiki ne ko magana, daga hakan akwai nuni da ƙarfe ko da da wasa ne; domin cewa Shaiɗan zai iya zaburar da hannunsa sai ya ƙawata masa dukan ɗan uwansa, ko ya fizge makamin daga hannunsa sai ya faɗa ba tare da zaɓinsa ba sai ya cutar da ɗan uwansa.
Toshe kafa da yin hani daga abinda zai kai zuwa abinda aka haramta.
Kwaɗayi akan zaman lafiyar zamantakewar jama'a da kiyaye alaƙoƙi tsakanin mutane, da rashin tsoratasu koda da nuni ne da kuma yi musu tsawa.
التصنيفات
Jinaya