Duk mayafin da ya yi ƙasa da idan sawu to yana cikin wuta

Duk mayafin da ya yi ƙasa da idan sawu to yana cikin wuta

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Duk mayafin da ya yi ƙasa da idan sawu to yana cikin wuta".

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargaɗi maza daga sakin dukkan abinda yake suturce jikinsu tufa ne ko wanduna ko waninsu ƙasa da idan sawun diga-digai, kuma abinda ke ƙasan idan sawu na ƙafar mai mayafin da ya sake shi to shi yana cikin wuta dan yi masa uƙuba akan aikinsa.

فوائد الحديث

Hani daga tsawaita tufa zuwa abinda ke ƙasa da idan sawu ga maza, kuma cewa hakan yana daga cikin manyan zunubai.

Ibnu Hajar ya ce: An togance abinda ya sake shi ƙasa dan lalurara daga sakin mayafi; misali kamar wanda idan sawunsa akwai ciwon da yake cutar da shi idan bai rufe shi da mayafin ba inda bai samu waninsa ba.

Wannan hukuncin ya keɓanci maza ne; domin cewa mata an umarcesu da su saki mayafansu ƙasa da idan sawu har zuwa tsawon zira'i.

التصنيفات

Kaya da kuma Ado