إعدادات العرض
Da a ce ana bawa mutane abu saboda ikirarin cewa nasu ne, da da yawa daga cikin mutane sun yi da'awar dukiyoyin wasu mutane da jinanansu, sai dai wanda duk ya yi da'awa to shi zai zo da shaidu, kuma rantsuwa tana kan wanda ya musanta
Da a ce ana bawa mutane abu saboda ikirarin cewa nasu ne, da da yawa daga cikin mutane sun yi da'awar dukiyoyin wasu mutane da jinanansu, sai dai wanda duk ya yi da'awa to shi zai zo da shaidu, kuma rantsuwa tana kan wanda ya musanta
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Da a ce ana bawa mutane abu saboda iƙirarin cewa nasu ne, da da yawa daga cikin mutane sun yi da'awar dukiyoyin wasu mutane da jinanansu, sai dai wanda duk ya yi da'awa to shi zai zo da shaidu, kuma rantsuwa tana kan wanda ya musanta».
الترجمة
العربية Español አማርኛ English اردو Indonesia বাংলা Français Türkçe Русский Bosanski සිංහල हिन्दी 中文 فارسی Tiếng Việt Tagalog Kurdî Português മലയാളം తెలుగు Kiswahili தமிழ் မြန်မာ ไทย Deutsch پښتو অসমীয়া Shqip Nederlands ગુજરાતી Кыргызча नेपाली Lietuvių دری Српски тоҷикӣ Kinyarwanda Magyar Čeština Moore Malagasy Oromoo ಕನ್ನಡ Wolof Azərbaycan O‘zbek Українська ქართული Македонски ភាសាខ្មែរ ਪੰਜਾਬੀ मराठी Kirundi Kurmancî Bahasa Melayuالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa da ace ana bawa mutane saboda kawai mujarradin da'awarsu ba tare da wasu dalilai ba ba kuma tare da wasu alamomi ba to da wasu mutane sun yi da'awar dukiyoyin wasu mutane da jinanensu, sai dai gabatar da shaida da dalili ya wajaba akan mai da'awa da abinda yake nema, idan ba shi da shaidu to sai a gabatar da da'awar akan wanda aka kawo karar, idan ya yi inkarinta to ya wajaba ya yi rantsuwa sai ya kubuta.فوائد الحديث
Ibnu Dakikil Id ya ce: Wanann Hadisin asali ne na hukunce-hukunce, kuma mafi girman makoma a lokacin jayayya da husuma.
Shari'a ta zo dan kare dukiyoyin mutane da jinanensu daga wasa.
Alkali ba ya hukunci da iliminsa kawai, yana komawa ne zuwa ga shaidu.
Dukkan wanda ya yi wata da'awa wacce ta wofinta daga hujja to ita abar watsarwa ce, daidai ne ta kasance a cikin hakkoki ne da mu'amaloli ko a cikin mas'alolin imani da sani.
التصنيفات
ƘARARRAKI DA SHEDU