Wanda ya karanta Ayatul kursiyyi a bayan kowacce sallar farilla to babu abinda zai hana shi shiga aljanna sai mutuwa

Wanda ya karanta Ayatul kursiyyi a bayan kowacce sallar farilla to babu abinda zai hana shi shiga aljanna sai mutuwa

Daga Abu Umamah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya karanta Ayatul kursiyyi a bayan kowacce sallar farilla to babu abinda zai hana shi shiga aljanna sai mutuwa".

[Ingantacce ne]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya karanta Ayatul Kursi bayan ƙare sallar farilla babu abinda zai hana shi shiga aljanna sai mutuwa; ita tana cikin Suratul Baƙara, faɗinSa - Maɗaukakin sarki -: {Allah, bãbu wani Ubangiji fãce Shi, Rãyayye, Wanda komai ya tsayu da Shi, gyangyaɗi bã ya kãma Shi, kuma barci bã ya kãma Shi, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa. Wanene wanda yake yin cẽto a wurinSa, fãce da izninSa? Yana sanin abin da yake a gaba gare su da abin da yake a bãyansu. Kuma bã su kẽwayẽwa da kõme daga ilminSa, fãce da abin da Ya so. KursiyyunSa ya yalwaci sammai da ƙasa. Kuma tsare su bã ya gajiyar da Shi, Kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma} [al-Baƙara: 255].

فوائد الحديث

Falalar wannan ayar mai girma; dan abinda ta ƙunsa na kyawawan sunaye, da siffofi Maɗaukaka.

An so karanta wannan ayar mai girma bayan kowacce sallar farilla.

Ayyuka na gari sababi ne na shiga aljanna.

التصنيفات

Zikirin Sallah