Lallai Qabari shi ne farkon Masauki daga cikin Masaukan Lahira, to idan Mutum ya tsira a cikinsa to babu abunda yafi sauqi kamar abu nagabansa, kuma idan bai tsira ba acikinsa to babu abunda ya fi shi tsanani.

Lallai Qabari shi ne farkon Masauki daga cikin Masaukan Lahira, to idan Mutum ya tsira a cikinsa to babu abunda yafi sauqi kamar abu nagabansa, kuma idan bai tsira ba acikinsa to babu abunda ya fi shi tsanani.

An rawaito daga Hani Maula Usman ya ce: Usman ya kasance idan ya tsaya kan Qabari yakanyi kuka har ya jiqa gemunsa, sai aka ce da shi: kana tuna Aljanna da Wuta baka yin kuka amma kuma kayi kuka da wannan? sai ya ce: lallai manzon Allah SAW ya ce: "Lallai Qabari shi ne farkon Masauki daga cikin Masaukan Lahira, to idan Mutum ya tsira a cikinsa to babu abunda yafi sauqi kamar abu nagabansa, kuma idan bai tsira ba acikinsa to babu abunda ya fi shi tsanani"

[Hasan ne] [Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi]

الشرح

Usman Bn Affan -Allah ya yarda da shi- ya kasance idan ya tsaya akan Kabari yankanyi Kuka har Gemunsa ya jiqe, sai aka ce da shi:kana tuna Aljanna da Wuta baka kuka amma kana kuka a Qabari? sai ya basu labarin cewa yaji Manzon Allah SAW yana bada Labari cewa Lallai Qabari shi ne farkon Masauki daga cikin Masaukan Lahira, to idan Mutum ya tsira a cikinsa to babu abunda yafi sauqi kamar abu nagabansa, kuma idan bai tsira ba acikinsa to babu abunda ya fi shi tsanani; Saboda idan yana da Zunubi to za'a kankare masa shi da da Azabar Qabari, in kuwa bai tsira ba a cikinsa, daga Azaba ko kuma a kankare masa Zunubansa da shi ya wanzu kan wani abu aknasa da ya cancanci Azaba to babu mafi tsanani kamar abunda yaje bayansa, Saboda Azabar Wuta ita ce Mafi tsanani

التصنيفات

Abubuwan tsoron cikin Qabari