Na tambayi Nana A'isha, na ce: Da wane abu Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yakasance yake farawa idan ya shiga gidansa? ta ce: Da asuwaki

Na tambayi Nana A'isha, na ce: Da wane abu Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yakasance yake farawa idan ya shiga gidansa? ta ce: Da asuwaki

Daga Shuraih ɗan Hani'i ya ce: Na tambayi Nana A'isha, na ce: Da wane abu Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yakasance yake farawa idan ya shiga gidansa? ta ce: Da asuwaki.

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Ya kasance daga shiriyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ne yana farawa da asuwaki idan ya shiga gidansa a kowane lokaci da daddare ko da rana.

فوائد الحديث

Halaccin yin asuwaki a game a dukkan lokuta, hakan yana ƙarfafa: A cikin lokutan da Shari’a ta so (a yi asuwaki) a cikinsu, daga garesu: A yayin shiga gida, da lokacin sallah, da lokacin alwala, da bayan farkawa daga bacci, da lokacin canjawar bashin baki.

Bayanin kwaɗayin tabi'ai akan tambaya game da halayen Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da sunnoninsa; dan su yi koyi da shi.

Ɗaukar ilimi daga ma'abotansa daga kuma wanda ya fi shi sani, inda aka tambayi Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - game da halin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a lokacin shiga gida.

Kyakkyawan mu'amalar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga iyalansa, inda ya kasance yana tsarkake bakinsa a lokacin shiga gida.

التصنيفات

Sunnonin Fixra