Lallai kada ɗayanku ya mutu sai yana kyautatawa Allah zato

Lallai kada ɗayanku ya mutu sai yana kyautatawa Allah zato

Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - kafin wafatinsa da (kwana) uku yana cewa: "Lallai kada ɗayanku ya mutu sai yana kyautatawa Allah zato".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar da musulmi cewa kar ya mutu sai shi yana kyautatawa Allah zato da rinjayarwarsa ɓangaren ƙauna a lokacin mutuwa da cewa Allah Zai yi masa rahama kuma Zai yi masa rangwame, domin cewa tsoro abin nema ne dan kyautata aiki, wancan halin ba halin ayyuka ba ne, abin nema a cikinsu (shi ne) rinjayar ƙauna.

فوائد الحديث

Kwaɗayin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan shiryarwar al'ummarsa, da tsananin tausayinsa da ita a dukkan halayenta; har a cikin rashin lafiyar rasuwarsa yana yi wa al'ummarsa nasiha kuma yana shiryar da ita akan hanyoyin tsira.

Al-Ɗaibi ya ce: Ku kyautata ayyukanku a yanzu har zatanku ga Allah ya kyautatu a lokacin mutuwa, domin cewa wanda ya munana aikinsa kafin mutuwa zatansa zai munana a lokacin mutuwa.

Mafi cikar halaye ga bawa (shi ne) daidaituwar ƙauna da tsoro, da kuma rinjayar so; soyayya ita ce abar hawa, ƙauna kuma mai korowa ce, tsoro kuwa mai tuƙawa ne, Allah kuma Mai sadarwa ne da baiwarSa da kuma karamcinSa.

Yana kamata ga wanda ya kasance makusanci daga wanda mutuwa ta halarto masa ya rinjayar da ɓangaren ƙauna da kyautatawa Allah zato, a cikin wannan hadisin cewa shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗi haka kafin ya rasu da (kwana) uku.

التصنيفات

Ayyukan Zukata