إعدادات العرض
«Lokacin da aka hau da ni (aka yi Mi'iraji da ni) na wuce wasu mutane da suke da farata na tagulla, suna yakusar fuskokinsu da ƙirazansu da su*, sai na ce: Su waye waɗannan ya Jibril, ya ce: Waɗanan sune waɗanda suke cin naman mutane, kuma suke afkawa cikin mutuncinsu».
«Lokacin da aka hau da ni (aka yi Mi'iraji da ni) na wuce wasu mutane da suke da farata na tagulla, suna yakusar fuskokinsu da ƙirazansu da su*, sai na ce: Su waye waɗannan ya Jibril, ya ce: Waɗanan sune waɗanda suke cin naman mutane, kuma suke afkawa cikin mutuncinsu».
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Lokacin da aka hau da ni (aka yi Mi'iraji da ni) na wuce wasu mutane da suke da farata na tagulla, suna yakusar fuskokinsu da ƙirazansu da su, sai na ce: Su waye waɗannan ya Jibril, ya ce: Waɗanan sune waɗanda suke cin naman mutane, kuma suke afkawa cikin mutuncinsu».
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Bahasa Indonesia Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Français ئۇيغۇرچە Kurdî Русский Tiếng Việt Magyar ქართული Kiswahili සිංහල Română অসমীয়া ไทย Portuguêsالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa shi: Lokacin da aka hau da shi zuwa sama a daren Isra'i da Mi'iraji, ya wuce wasu mutane suna da farata na tagulla suna yakusa suna yayyaga fuskokinsu da ƙirazansu da su, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya tambayi (Mala’ika) Jibril - aminci ya tabbata agare shi -: Me waɗannan mutanen suka aikata har ake musu sakayya da wannan azabar? Sai (Mala’ika) Jibril - aminci ya tabbata agare shi - ya ce: Waɗanan sune waɗanda suke yi da mutane, kuma suke magana a kan mutuncinsu ba tare da gaskiya ba.فوائد الحديث
Gargaɗarwa mai tsanani daga yi da mutum, da kuma kamanta mai yi da mutum da wanda yake cin naman 'dan Adam.
Afkawa cikin mutuncin mutane yana daga yi da mutum da makamancinsa na manyan zunubai.
Al-Ɗaibi ya faɗa a cikin faɗinsa: "Suna yakusa", ya ce: Yayin da yakusar fuska da ƙirji suka zama daga cikin siffofin mata masu kukan mutuwa sai aka sanya hakan sakayyar wanda yake yi da mutane, kuma yake cin mutuncin musulmai, dan sanarwa da cewa su ba sa daga cikin siffofin maza, kai su suna daga cikin siffofin mata a cikin mafi munin hali kuma mafi munin sura.
Wajabcin yin imani da gaibu da kuma dukkanin abinda Allah da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suka bada labari da shi.
التصنيفات
Zargin Savo