«Ka taimaki ɗan'uwanka azzalimi ko wanda aka zalinta»*. …

«Ka taimaki ɗan'uwanka azzalimi ko wanda aka zalinta»*. Sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah, zan taimake shi idan ya kasance wanda aka zalinta ne, shin kana ganin idan ya zama azzalimi ta yaya zan taimake shi? ya ce: «Ka kare shi - ko ka hana shi - daga zalinci; domin cewa hakan taimakonsa ne».

Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ka taimaki ɗan'uwanka azzalimi ko wanda aka zalinta». Sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah, zan taimake shi idan ya kasance wanda aka zalinta ne, shin kana ganin idan ya zama azzalimi ta yaya zan taimake shi? ya ce: «Ka kare shi - ko ka hana shi - daga zalinci; domin cewa hakan taimakonsa ne».

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci musulmi da ya taimaki ɗan'uwansa musulmi, daidai ne ya kasance azzalimi ne ko wanda aka zalinta, sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah, zan taimake shi idan ya kasance wanda aka zalinta ne, shi ne in hana a zalince shi, shin kana ganin idan ya zama azzalimi ta yaya zan taimake shi? Ya ce: Ka hana shi ka yi riƙo da hannunsa ka kare shi, ka hana shi zalincin; domin hakan shi ne taimakonsa akan Shaiɗaninsa da kuma ransa mai umartarsa da mummunan aiki.

فوائد الحديث

Faɗakarwa akan wani haƙƙi daga cikin haƙƙoƙin 'yan uwantaka ta imani tsakanin musulmai.

Riƙo da hannun azzalimi, da kuma hana shi zalinci.

Yadda Musulunci ya saɓawa fahimce-fahimcen Jahiliyya, inda suka kasance suna taimakekeniya, duk ɗayane sun kasance waɗanda aka zalinta ne ko masu zalintar wasunsu ne.

التصنيفات

Al-ummar Musulmai