إعدادات العرض
Ya Abu Zarr idan zaka dafa romo to ka yawaita ruwansa, ka bibiyi maƙotanka da shi
Ya Abu Zarr idan zaka dafa romo to ka yawaita ruwansa, ka bibiyi maƙotanka da shi
Daga Abu Zarr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ya Abu Zarr idan zaka dafa romo to ka yawaita ruwansa, ka bibiyi maƙotanka da shi".
[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Kurdî Tiếng Việt Nederlands Kiswahili অসমীয়া ગુજરાતી සිංහල Magyar ქართული Românăالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitarwa Abu Zarr al-Gifari - Allah Ya yarda da shi - cewa idan zai dafa romo to ya yawaita ruwansa, ya bibiyi maƙotansa da shi.فوائد الحديث
Kwaɗaitarwa akan kyakkyawar mu'amala tare da maƙota.
An so yin kyauta tsakanin maƙota; domin hakan yana gadar da soyayya kuma yana ƙara ƙauna, wannan kyautar tana ƙarfafuwa idan abincin yana da ƙanshi, kuma an san buƙatuwar maƙoci (gare shi).
Kwaɗaitarwa akan bada abin alheri da abinda ya sawwaƙa daga gare shi koda kaɗan ne, da shigar da farin ciki ga musulmai.
التصنيفات
Sulhu da Hukunce Hukuncen Maqwabtaka