Lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aika shi zuwa Yaman sai ya umarce shi ya karɓi Tabi'i namiji ko mace (wanda yake bin uwarsa kiwo) daga dukkan (shanu) talatin

Lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aika shi zuwa Yaman sai ya umarce shi ya karɓi Tabi'i namiji ko mace (wanda yake bin uwarsa kiwo) daga dukkan (shanu) talatin

Daga Mu'az - Allah Ya yarda da shi -: Lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aika shi zuwa Yaman sai ya umarce shi ya karɓi Tabi'i namiji ko mace (wanda yake bin uwarsa kiwo) daga dukkan (shanu) talatin, haka (ya karɓi) Musinnah daga dukkanin (shanu) arba'in, daga (ya karɓi) dinari ɗaya ko kwatankwacinsa na Ma'afir wasu tufa ne na Yaman daga duk wanda ya isa mafarki.

[Ingantacce ne a baki dayan Riwayoyin sa]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aika Mu'az ibnu Jabal - Allah Ya yarda da shi - zuwa Yaman dan koyar da mutane da kuma kiransu, daga cikin abin da ya umarce shi da shi shine ya karɓi Zakkar shanunsu tabi'i ɗaya namiji ko mace daga dukkanin talatin; shine wanda ya cika shekara ɗaya, haka (ya karɓi) Musinna daga dukkanin arba'in; ita ce wacce ta cika shekara biyu. Kuma ya karɓi jizyar dinari ɗaya daga mazowa littafi Yahudawa da Nasara daga dukkanin namiji baligi, ko abin da ya yi daidai da dinari ɗaya na tufafin Yaman waɗanda ake kiransu da: Ma'afirri.

فوائد الحديث

Ba'a karɓar jizya sai daga wanda ya isa mafarki; domin cewa ƙa'idar wanda ba'a karɓa daga gare shi ita ce: Shine wanda ba ya halatta a kashe shi idan an ribace shi: Daga ƙaramin yaro, da mace, da wasunsu.

Ƙimanta jizyar yana komawa ne ga ijtihadin liman, domin ita tana saɓawa gwargwadan saɓawar guri da kuma zamani, da wadata da kuma talauci, dalili akan haka cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ne wanda ya ƙaddara gwargwadanta ga mutanen Yaman, sai ya ce wa Mu'az; "Ka karɓi dinari ɗaya daga dukkanin wanda ya isa mafarki" yayin da jizya ta ƙaru lokacin Umar - Allah Ya yarda da shi - ya ƙayyade gwargwadanta ga mutanen Sham.

Himmatuwa da tara Zakkah, da kuma wakilta wanda zai tattarota yana daga cikin muhimman ayyukan shugaba.

Tabi'i: Shi ne wanda ya cika shekara ɗaya, ya shiga cikin shekara ta biyu, kuma an ambace shi tabi'i ne; domin shi bai gushe ba yana bin uwarsa kiwo.

Dinari: Kuɗi ne na zinari, dinari na Musulunci: Awonsa shine Gram huɗu da rubu'in zinari (4.25GM).

التصنيفات

Zakkar Dabbobi