إعدادات العرض
Zuciyar babba ba zata gushe ba tana budurwa a kan abubuwa biyu: A son duniya da tsawon buri
Zuciyar babba ba zata gushe ba tana budurwa a kan abubuwa biyu: A son duniya da tsawon buri
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Zuciyar babba ba zata gushe ba tana budurwa a kan abubuwa biyu: A son duniya da tsawon buri".
الترجمة
العربية Tiếng Việt Bahasa Indonesia Nederlands Kiswahili English অসমীয়া ગુજરાતી සිංහල Magyar ქართული Românăالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa dattijo yana girma jikinsa yana rauni, sai dai zuciyarsa budurwa ce akan son abubuwa biyu: Na farko: Son duniya da yawan dukiya. Na biyu: Tsawon rayuwa da shekaru da buri.فوائد الحديث
Bayanin abinda aka halicci mutum a kansa, shi ne son duniya da tsawon buri.
Nuni akan zargin yawan buri, da kwaɗayi akan tara dukiya, hakan yana hukunta tanadi ga mutuwa da falalar sadaka ga mawadaci, da kamewa ga talaka.
Mafi soyuwar abubuwa ga ɗan Adam shi ne ransa, shi mai kwaɗayi ne a akan wanzuwarsa, saboda haka sai ya so tsawon rayuwa, kuma ya so dukiya; domin cewa shi yana daga mafi girman sabubba a dawwamar lafiya da jin daɗi, a duk lokacin da ya ji kusancin ƙarewar hakan sai sonsa gare shi ya tsananta, da kuma kwaɗayinsa a kan dawwamarsa.
التصنيفات
Zargin Son Duniya