إعدادات العرض
Ku yawaita tina mai rushe jin daɗi". Yana nufin mutuwa
Ku yawaita tina mai rushe jin daɗi". Yana nufin mutuwa
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ku yawaita tina mai rushe jin daɗi". Yana nufin mutuwa.
[Hasan ne] [رواه الترمذي والنسائي وابن ماجه]
الترجمة
العربية Tiếng Việt Bahasa Indonesia Nederlands Kiswahili English অসমীয়া ગુજરાતી සිංහල Magyar ქართული Română ไทย Português मराठी ភាសាខ្មែរ دری አማርኛ বাংলা Kurdî తెలుగు Македонски Tagalog Українська ਪੰਜਾਬੀ മലയാളം Mooreالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar akan yawaita tinanin mutuwa, da tinaninta ne mutum yake tuna lahira, kuma soyayyarsa ga duniya ta rushe a cikin zuciyarsa, musammanma dai abubuwan da aka haramta.فوائد الحديث
Mutuwa tana yanke jin daɗin duniya, sai dai a haƙƙin mumini tana dago shi zuwa jin daɗin lahira da jin daɗin aljanna da abinda yake faruwa a cikinta na alheri mai girma.
Tina mutuwa da abinda ke bayanta yana daga sabubban tuba da barin laifi da kuma tanadi dan lahira.
التصنيفات
Zargin Son Duniya