(Mutum) bakwai Allah - Maɗaukakin sarki - Zai inuwantar da su a cikin inuwarSa ranar da babu wata inuwa sai inuwarSa

(Mutum) bakwai Allah - Maɗaukakin sarki - Zai inuwantar da su a cikin inuwarSa ranar da babu wata inuwa sai inuwarSa

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «(Mutum) bakwai Allah - Maɗaukakin sarki - Zai inuwantar da su a cikin inuwarSa ranar da babu wata inuwa sai inuwarSa: Shugaba adali, da saurayin da ya taso a cikin bautar Allah, da mutumin da zuciyarsa ta rataya da masallatai, da mutum biyu da suka so juna saboda Allah, sun haɗu saboda Shi kuma suka rabu saboda Shi, da mutumin da mace mai matsayi da kyau ta neme shi sai ya ce: Lallai ni ina jin tsoron Allah, da mutumin da ya yi sadaka sai ya ɓoyeta har (hannunsa) na hagu bai san abinda (hannunsa) na dama ya ciyar ba, da mutumin da ya ambaci Allah shi kaɗai sai idanuwansa suka zubar da hawaye».

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa nau'i bakwai na muminai bushara cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Zai inuwantar da su a inuwar al-ArshinSa a ranar da babu wata inuwa sai inuwarSa: Na farko: Shugaba adali a kansa ba fasiƙi ba, kuma mai adalci tsakanin talakawansa ba azzalimi ba; shi ne babban shugaba, dukkan wanda ya jiɓinci wani abu na al'amuran musulmai sai ya yi adalci a cikinsa zai risku da hakan. Na biyu: Saurayin da ya taso a cikin bautar Allah, kuma ya ƙarar da samartakarsa da nishaɗinsa, har ya mutu akan hakan. Na uku; Mutumin da zuciyarsa ta rataya da masallaci idan ya fita daga cikinsa har sai ya dawo zuwa gare shi, saboda tsananin soyayyarsa gare shi da kuma lazimtar masallacin da ci gaba da kasancewa a cikinsa da zuciya, koda wani abu mai bijirowa ya bijirowa jiki (kamar rashin lafiya) kuma ya zama a wajen masallacin. Na huɗu; Mutum biyu kowane ɗaya daga cikinsu ya so ɗayan saboda Allah a haƙiƙa, kuma suka dawwama akan soyayyar Addini wani abu mai bijirowa na duniya bai rabasu ba daidai ne sun haɗu a haƙiƙa ko a'a har mutuwa ta rabasu. Na biyar: Da mutumin da mace ta neme shi akan kanta dan aikata alfasha, kuma mai asali ce da ɗaukaka da matsayi da alfarma da dukiya da kyau, sai ya ƙi kuma ya ce: Ni ina jin tsoron Allah. Na shida: Mutumin da ya yi sadaka kaɗan ce ko mai yawa bai yi riya a cikinta ba kai ya ɓoyeta har hagunsa bata sanin abinda damansa take ciyarwa. Na bakwai: Mutumin da ya ambaci Allah da zuciyarsa daga tinani ne, ko da harshensa na zikiri, a keɓance daga mutane sai hawaye suka kwaranyo daga idanuwansa dan jin tsoron Allah da kuma girmama Shi - Maɗaukakin sarki -.

فوائد الحديث

Falalar nau'i bakwan da aka mabata da kwaɗaitarwa akan koyi da su.

Ibnu Hajar ya ce a cikin faɗinsa: "A cikin inuwarSa": An ce abinda ake nufi: Inuwar Al’arshinsa, Hadisin Salman yana nuni a kansa daga (riwayar) Sa'id ɗan Mansur da Isnadi kykkyawa: "Mutum bakwai Allah Zai inuwantar da su a cikin inuwar al-ArshinSa".

Ibnu Hajar ya ce: Mafi kyan abinda aka fassara mai adalci da shi cewa shi ne wanda yake bin umarnin Allah ta hanyar ajiye kowane abu a bigiransa ba tare da wuce gona da iri ko sakaci ba, kuma ya gabatar da shi a ambato dan gamewar amfanin da shi.

Falalar jiran sallah bayan sallah.

Nawawi ya ce: A cikinsa akwai kwaɗaitarwa akan soyayya saboda Allah da bayanin girman falalarta.

An keɓanci matsayi da kyau dan tsananin kwaɗayin mutane a cikinsu da kuma kwaɗayinsu a kansu, da wahalar samunsu.

Abinda ya fi a sadaka shi ne ɓoyewa da nisanta daga riya, duk da an halatta bayyanar da sadaka da zakka idan sun kuɓuta daga riya kuma aka nufi kwaɗaitar da wani akan ciyarwa kuma dan waninsa ya yi koyi da shi, da kuma bayyanar da alamomin Musulunci.

Kaɗai waɗannan mutum bakwan sun samu wannan ni'imar ce saboda ikhlasi ga Allah - Maɗaukakin sarki - da kuma saɓawa son rai.

Faɗinsa: "Mutum bakwai Allah Zai inuwantar da su": Taƙaitawarsu da wannan adadin ba abin nufi bane, kai wasun waɗannan nau'ikan sun zo a cikin hadisin daga waɗanda Allah Zai inuwantar da su a inuwar Al’ArshinSa.

Ibnu Hajar ya ce: Ambatan maza a cikin hadisin ba shi da wani abin fahimtar cewa su ake nufi kawai; kai mata ma suna tarayya tare da mazan a cikin ayyuka a abinda aka ambata, sai dai idan ana nufin shugaba adali wato babban shugabanci, inba haka ba to mace zata iya shiga tunda itama tana da iyalai kuma ta yi adalci a cikinsu, kuma ɗabi'ar lazimtar masallaci ta fitar da mace; domin cewa sallar mace a cikin gidanta ya fi ta yi a masallaci, abinda ke koma bayan hakan to tarayya da su ta tabbata, har namijin da mace ta neme shi shima ana suranta samun hakan a macen da sarki kyakkyawa ya nemeta a misali sai taƙi dan jin tsoron Allah - Madaukakin sarki - tare da cewa tana bukatar hakan.

التصنيفات

Fa’idojin Ambaton Allah Maigirma da xaukaka, Tsarkake Zuciyoyi, Hukunce Hukuncen Masallaci