‌Lallai kada tsoron mutane ya hana ɗayanku faɗin gaskiya idan ya ganta ko ya santa

‌Lallai kada tsoron mutane ya hana ɗayanku faɗin gaskiya idan ya ganta ko ya santa

Daga Abu sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Lallai kada tsoron mutane ya hana ɗayanku faɗin gaskiya idan ya ganta ko ya santa».

[Ingantacce ne]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa sahabbansa huɗuba, daga cikin abinda ya yi musu wasicci da shi cewa kada tsoro da kwarjinin mutane da kuma ƙarfinsu ya hana musulmi faɗin gaskiya ko umarni da ita idan ya ganta ko ya santa.

فوائد الحديث

Kwaɗaitarwa akan bayyanar da gaskiya da kuma rashin ɓoyeta dan jin tsoron mutane.

Faɗin gaskiya ba ya nufin rashin lazimtar ladabi ta hanyar faɗinta da kuma hikima da kyakkyawan wa'azi a cikinta.

Wajabcin inkarin munkari, da kuma gabatar da haƙƙin Allah - Maɗaukakin sarki - akan mas'lahohin mutane waɗanda sukaci karo da ita.

التصنيفات

Hukuncin Umarni da kyakkyawan aiki da hani da Mummunan aiki