إعدادات العرض
Gangaran a karatun Alƙur'ani yana tare da manyan mala'iku masu biyayya ga Allah, kuma wanda yake karanta Alƙur'ani kuma yake guragura a cikinsa yana mai shan wuya to yana da lada biyu
Gangaran a karatun Alƙur'ani yana tare da manyan mala'iku masu biyayya ga Allah, kuma wanda yake karanta Alƙur'ani kuma yake guragura a cikinsa yana mai shan wuya to yana da lada biyu
Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Gangaran a karatun Alƙur'ani yana tare da manyan mala'iku masu biyayya ga Allah, kuma wanda yake karanta Alƙur'ani kuma yake guragura a cikinsa yana mai shan wuya to yana da lada biyu.
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Bahasa Indonesia Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Français සිංහල Kurdî Português Русский Tiếng Việt Kiswahili Nederlands অসমীয়া ગુજરાતી Magyar ქართული Românăالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda yake karanta Alƙur'ani, alhali shi mai kyakkyawar hadda ne mai kyautatawa, kuma gwani haziƙi a karanta shi, to a lahira yana da ladan da zai zama a matsayinsa tare da manyan mala'iku matafiya masu karamci. Kuma wanda yake karanta Alƙur'ani yake guragura a cikinsa yana kaikawo a karanta shi; dan raunin haddarsa alhali shi tare da hakan yana riƙe da shi, kuma yana wahalar da shi to shi yana da lada biyu; ladan karatun Alkur'ani da kuma ladan wahala da kaikawo a cikin karanta shi.فوائد الحديث
Kwaɗaitarwa akan haddace Alƙur'ani da kyautata shi da yawaita karanta shi dan samun lada da sakamako, da kuma bayanin ɗaukakar matsayin wanda ya aikata hakan.
Alƙali ya ce: Ba wai ma'anarsa cewa wanda yake guragura gurin karanta shi ya fi gwani lada ba, kai gwani ya fi yawan lada; domin shi gwani yana tare da mala'iku matafiya kuma yana da ladaddaki mai yawa, kuma bai ambaci wannan matsayin ga waninsa ba, to kuwa ta yaya wanda bai kula da Littafin Allah - Maɗaukakin sarki - ba da haddace shi da kyautata shi da yawan karanta shi da dirayarsa hakikanin kulawarsa har ya zama gwani a cikinsa zai riske shi.
Ibnu Baaz ya ce: Wanda yake karanta Alƙur'ani alhali shi gwani ne a cikinsa, yana kyautata karatunsa, kuma yana haddarsa da kyau yana tare da mala'iku matafiya masu daraja, yana nufin: Idan ya kasance yana karanta shi a faɗa da aiki, ba wai mujarradin karantawar kawai ba, yana kyautata karatunsa kuma yana aiki da shi, shi yana tsaye da shi a lafazi da ma'ana.