إعدادات العرض
Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance ba ya barin (raka'o'i) huɗu kafin azahar da raka’a biyu kafin sallar (Asuba)
Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance ba ya barin (raka'o'i) huɗu kafin azahar da raka’a biyu kafin sallar (Asuba)
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah ya yarda da ita -: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance ba ya barin (raka'o'i) huɗu kafin azahar da raka’a biyu kafin sallar (Asuba).
[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Bahasa Indonesia Tagalog Türkçe اردو हिन्दी Français 中文 Kurdî Português Русский Nederlands Tiếng Việt অসমীয়া ગુજરાતી Kiswahili አማርኛ پښتو සිංහල ไทย മലയാളം नेपालीالشرح
Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana lazimta akan sallolin nafilfili a ɗakinta kuma ba ya barinsu: Raka'o'i huɗu da sallama biyu kafin sallar Azahar, da kuma raka'o'i biyu kafin sallar Asuba.فوائد الحديث
An so kiyayewa akan raka'o'i huɗu kafin sallar Azahar, da raka'a biyu kafin sallar Asuba.
Abinda ya fi shi ne ka sallaci (salloli) ratibai a cikin gida, da haka ne Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta bada labari.
التصنيفات
Sunnoni Ratibai