Manzon Allah tsira da amincin Allah ya shigo wajen mu lokacin da y'arsa Zainab ta rasu, sai ya ce: ku wanke ta sau uku ko sau biyar, ko fiye da haka - gwargwadon yadda kuka ga ya dace - ku sanya ruwa da magarya, sannan ku sa kafur - ko wani abu na kafur - in kun kammala ku sanar da ni.

Manzon Allah tsira da amincin Allah ya shigo wajen mu lokacin da y'arsa Zainab ta rasu, sai ya ce: ku wanke ta sau uku ko sau biyar, ko fiye da haka - gwargwadon yadda kuka ga ya dace - ku sanya ruwa da magarya, sannan ku sa kafur - ko wani abu na kafur - in kun kammala ku sanar da ni.

Daga Ummu Adiyya Al'ansariyya -Allah ya yarda da ita- tace:"Manzo tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya shigo wajenmu a lokacin da 'yarsa Zainab ta rasu,sai yace:kuyi mata wanka da ruwa da magarya sau uku ko biyar,ko fiyema da haka in kun ga dacewar hakan,ku sanya kafur a wankan karshe.sai ya bamu kwarjallensa,yace ku rufeta da shi.Awata ruwayar"ko sau bakwai"ya kara da cewa:"ku fara da damanta da kuma gurar alwalla" Ummu Adiyya tace: sai muka yi mata tufka uku a kanta".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Yayin da Zainab 'yar Manzon Allah ta rasu, sai ya shiga wajen masu yi mata wanka, acikinsu akwai Ummu Adiyya Al'ansariyya donyakowyarda su yadda ake wanka, don ta isa zuwa ga ubangijinta a tsarkake cikin tsafta,sai yace:ku wanke ta sau uku, ko sau buyar, ya zama karshen wankanta wutiri ne, in kun ga alamar bukatar yin haka. don jikin ya fita fes ku sanya ruwa da magarya, ku sanya kafur daga karshe don ta zama tana kanshin turare, kuma sa jikinta ya yi kwari.sai yayi musu wasiyya da su fara da gabobinta mafiya daraja kuma su fara da damanta,kuma ya umarce su in sun kammala su sanar dashi,bayan da suka kammala sai suka sanar da shi,sai ya basu kwarjallan shi wanda ya shafi jikinsa mai tsarki,don su rufa mata shi,don yazame mata albarka a kabarinta, masu yiwa Zainab wanka su warware gashin kanta suka wanke shi sannan suka yi masa tufka uku daya a gaba biyu a gefe da gefe suka kuma mayar da su baya

التصنيفات

Wankan Gawa