Da ba dan kar na tsanantawa muminai ba - ko ga: al'ummata ba - dana umarce su da yin asuwaki a yayin kowace sallah

Da ba dan kar na tsanantawa muminai ba - ko ga: al'ummata ba - dana umarce su da yin asuwaki a yayin kowace sallah

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Da ba dan kar na tsanantawa muminai ba - ko ga: al'ummata ba - dana umarce su da yin asuwaki a yayin kowace sallah".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa shi da ba dan tsoron wahala ga muminai daga al'ummarsa ba da ya wajabta musu yin anfani da asuwaki tare da kowace sallah.

فوائد الحديث

Tausayin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga al'ummarsa, da kuma tsoron wahala akansu.

Asali a umarnin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - (shi ne) wajabci, sai dai inda dalili ya tsayu akan cewa shi nafila ne.

An so yin asuwaki da kuma (bayanin) falalarsa a yayin kowace sallah.

Ibnu Daƙiƙul id ya ce: Hikima a mustahabbacin asuwaki a yayin tashi zuwa sallah (shi ne) kasancewarta halin neman kusanci ne zuwa ga Allah, sai ya hukunta ka zama a halin cika da tsafta dan bayyanar da ɗaukakar ibada.

Gamewar hadisin ya ƙunshi asuwaki ga mai azimi koda bayan zawali ne, kamar salloli biyu: Azahar da la'asar.

التصنيفات

Rayuwar Manzon Allah