Shin ana taimakonku ne ko ana azurtaku sai saboda raunananku

Shin ana taimakonku ne ko ana azurtaku sai saboda raunananku

Daga Mus'ab ɗan Sa'ad ya ce: Sa'ad - Allah Ya yarda da shi - ya ga cewa shi yana da wata falala akan wanda ke ƙasa da shi, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shin ana taimakonku ne ko ana azurtaku sai saboda raunananku".

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi]

الترجمة

ar bn bs en es fa fr id ru tl tr ur zh hi vi ug ku nl sw as gu si hu ka ro

الشرح

Sa'ad ɗan Abu Waƙas - Allah Ya yarda da shi - ya yi zatan cewa shi yana da wata falala akan wanda ke ƙasa da shi daga raunana saboda gwarzantakarsa da makamancin haka! Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Shin ana taimakonku ne kuma ana azirtaku ai sai saboda raunananku ta hanyar addu'o'insu da sallalolinsu da ikhlasinsu; domin su a galibi su ne mafi tsananin ikhlasi a cikin addu'a, kuma mafi yawan khushu'i a cikin ibada dan wofintar zuciyarsu daga rataya da ƙawace-ƙawacen duniya.

فوائد الحديث

Kwaɗaitarwa akan tawali'u da hana rena wasu daban.

Ibnu Hajar ya ce: Idan mai ƙArgo yana rinjaya saboda gwarzantakara, to shi mai rauni yana rinjaya saboda falalar addu'arsa da kuma ikhlasinsa.

Kwaɗaitarwa akan kyautatawa talakawa da basu haƙƙoƙinsu, domin hakan yana daga sabubban rahamar Allah gareka da kuma taimakonSa.

التصنيفات

Halayen Mutane na Qwarai