bayan kowace sallah kada ka bar faɗin: Ya Allah Ka taimakeni akan ambatanKa da gode maKa da kyakkyawar ibadarKa

bayan kowace sallah kada ka bar faɗin: Ya Allah Ka taimakeni akan ambatanKa da gode maKa da kyakkyawar ibadarKa

Daga Mu'az Bin Jabal -Allah Ya yarda da shi -: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe hannuna, sai ya ce: "Ya Mu'az, wallahi lallai ni ina sonka", sai ya ce: "Ina yi maka wasicci ya Mu'az bayan kowace sallah kada ka bar faɗin: Ya Allah Ka taimakeni akan ambatanKa da gode maKa da kyakkyawar ibadarKa".

[Ingantacce ne]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe hannun Mu'aza - Allah Ya yarda da shi -, sai ya ce masa: Wallahi lallai ni ina sonka, kuma ina yi maka wasicci ya Mu'az a ƙarshen kowace sallah kada kabar faɗin: (Ya Allah Ka taimakeni akan ambatanKa) a kowace magana da aikin da zai kusanto da ni zuwa biyayya, (da godiyarKa) ta hanyar samun ni'imomi da tunkuɗe masifu, (da kyakkyawar bautarKa) ta hanyar yin ikhlasi ga Allah da bin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

فوائد الحديث

Halaccin baiwa mutum labari da sonsa a lamarin Allah.

An so yin wannan addu'ar a bayan kowace sallar farilla da nafila.

A cikin yin addu'a da waɗannan lafuzan 'yan kaɗan (akwai) abbuwan nema a duniya da lahira.

Daga fa'idojin soyayya a lamarin Allah yin wasicci da gaskiya da yi wa juna nasiha da taimakekeniya akan aikin alheri da tsoron Allah.

Malam al-Ɗaibi ya ce: Ambatan Allah shi ne kan gaba a buɗewar ƙirji, godiyarSa kuma tsani ce na ni'imomi ababen amsawa, kyakkyawar ibada kuwa abar nema daga gare shi, shi ne nisantar abinda zai shagaltar da shi daga Allah - Maɗaukakin sarki -.

التصنيفات

Zikirin Sallah