Allah Ya ce: Dukkan aikin ɗan Adam nasa ne, sai azimi, lallai shi nawa ne kuma nine zan yi sakayya da shi

Allah Ya ce: Dukkan aikin ɗan Adam nasa ne, sai azimi, lallai shi nawa ne kuma nine zan yi sakayya da shi

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Allah Ya ce: Dukkan aikin ɗan Adam nasa ne, sai azimi, lallai shi nawa ne kuma nine zan yi sakayya da shi, azimi garkuwa ne, idan yinin azimin ɗayanku ya kasance to kada ya yi kwarkwasa kada ya yi zancen banza, idan wani ya zage shi ko ya yi faɗa da shi, to ya ce lallai ni mai azimi ne, na rantse da wanda ran (Annabi) Muhammad yake a hannunSa, bashin bakin mai azimi shi ne mafi ɗaɗi a wurin Allah daga ƙanshin almiski, mai azimi yana da farin ciki biyu da zai yi farin ciki da su: Idan zai yi buɗa baki zai yi farin ciki, kuma idan ya gamu da Ubangijinsa zai yi farin ciki da aziminsa".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Yana faɗa a cikin Hadisi Ƙudsi: Dukkan aikin Ɗan Adam ana ninka kyakkyawa da kwatankwacinsa goma zuwa ninki ɗari bakwai, sai azimi; shi nawa ne riya ba ta shiga cikinsa, kuma nine zan yi sakayya da shi sai in kaɗaita da sanin gwargwadan ladansa da kuma ninka kyawawan (ladansa). Sannan Ya ce: (Azimi garkuwa ne) kuma kariya ne kuma sitira ne kuma katanga ne mai katangewa daga wuta; domin cewa shi kamewa ne daga sha'awowi da afkawa cikin zunubai, wuta kuma abar kewayewa ce da sha'awowi. (Idan yinin azimin ɗayanku ya kasance to kada ya yi kwarkwasa) da yin jima'i da abubuwan gabatarwarsa, ko mummunan zance kai tsaye. (Kada ya yi zancen banza) da yin husuma da kuma kururuwa. (Idan wani ya zage shi ko ya yi faɗa da shi) a cikin Ramadan to ya ce: Lallai ni mai azimi ne; wataƙila ya ƙyale shi, idan ya nace sai dai faɗa to a haƙiƙa to sai ya tunkuɗe shi da mafi sauƙi, sai mafi sauƙi kamar wanda ya shigo maka gida. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi rantsuwa da wanda ransa yake a hannunSa cewa canzawar bashin bakin mai azimi saboda azimin ya fi daɗi a wurin Allah ranar alƙiyama daga ƙanshin almiski a wurinku, kuma ya fi yawan lada daga almiski abin so gare shi a ranakun juma'a da kuma majalisan zikiri. Mai azimi yana da farin ciki biyu da zai yi farin ciki da su: Idan zai yi buɗa baki zai yi farin ciki da gushewar yunwarsa da kuma ƙishirwarsa saboda yadda aka halatta masa buda baki. Kuma zai yi farin ciki da cikar aziminsa da kuma kammala bautarsa, da kuma sauƙi daga Ubangijinsa, da taimako akan aziminsa na gaba. (Idan ya gamu da Ubangijinsa zai yi farin ciki da aziminsa) da sakamakonsa da kuma ladansa.

فوائد الحديث

Falalar azimi kuma cewa shi yana kiyaye maishi a duniya daga sha'awowi, a lahira kuma daga azabar wuta.

Daga ladubban azimi barin zancen alfasha da zancen banza, da kuma haƙuri akan cutar mutane da fuskantar munanawarsu da yin haƙuri da kuma kyautatawa.

Mai azimi ko mai ibada idan ya yi farin ciki saboda cikar bautarsa da kuma ƙarewa daga gareta to hakan ba zai tauye ladansa a lahira ba.

Cikakken farin ciki shi shi da haɗuwa da Allah - Maɗaukakin sarki -, lokacin da ake cika wa masu haƙuri da masu azimi ladansu ba tare da hisabi ba.

Sanar da mutane aikin ɗa'a a lokacin buƙata da maslaha ba ya daga cikin riya saboda faɗinsa: (Lallai ni mai azimi ne).

Mai azimin da ya cika aziminsa shi ne wanda gaɓɓansa suka yi azimi daga zunubai, kuma harshensa daga ƙarya da alfasha, da faɗin zur, cikinsa kuma daga abin ci da abin sha.

Karfafawar hani daga zancen banza da husuma da ihu a lokacin azimi, inba haka ba to wanda ba ya azimi ma an hana shi hakan.

Wannan hadisin yana daga abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yake ruwaito shi daga Ubangijinsa, ana ambatonsa da Hadisi Ƙudsi, ko Ilahi, shi ne wanda lafazinsa da ma'anarsa daga Allah ne, sai dai cewa shi babu abubuwan da Alƙur’ani ya keɓannta da su a cikinsa, waɗanda ya keɓanta da su daga waninsa, kamar bauta da karanta shi, da yin tsarki sabo da shi da I’IJAZ (ƙalubalanta) da gajiyarwa, da sauransu.

التصنيفات

Falalar Azumi