Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce mini: «Ka yi mini karatu

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce mini: «Ka yi mini karatu

Daga Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce mini: «Ka yi mini karatu» Na ce: Ya Manzon Allah, shin na yi maka karatu, alhali kai aka saukarwa? Ya ce: «Eh» sai na karanta Surat al-Nisa'i har sai da na zo wannan ayar: {To yaya al'amarin zai kasance idan muka zo da kowace al'umma tare da mai yi mata shaida, kai kuma Muka zo da kai a matsayin mai shaida kan waɗannan al'ummar?”. {al-Nisa'i 41]. ya ce: «Ya isa haka» sai na juya gurinsa, sai ga idanuwansa suna zubar da hawaye.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nemi Abdullahi Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya karanta masa wani abu na Alƙur'ani, sai ya ce; Ya Manzon Allah, ta yaya zan karanta maka alhali kai aka saukarwa?! sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Lallai ni ina son in ji shi daga wanina, sai ya karanta masa Suratu al-Nisa'i yayin da ya kai ga faɗinSa Allah - Maɗaukakin sarki -:{To yaya al'amarin zai kasance idan Muka zo da kowace al'umma tare da mai yi mata shaida, kai kuma Muka zo da kai a matsayin mai shaida akan waɗannan al'ummar?} Wato yaya halinka da halin al'ummarka zasu kasance idan Muka zo da kai kana mai shaida ga al'ummarka cewa kai ka isar musu da saƙo, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ka tsaya da karatun a yanzu, Ibnu Mas'uda - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Sai na juya wajensa sai ga idanuwansa suna zubar da hawaye dan tsoron mauƙifin (alƙiyama), da kuma tausayin al'ummarsa.

فوائد الحديث

Nawawi ya ce: An so sauraren Alƙur'ani da karkata zuwa gare shi da kuka a wurin karatun, da kuma la’akari da ma'anoninsa, kuma an so neman karantawa daga waninsa dan ya saurare shi, kuma hakan ya fi kai matuƙa a fahimta da kuma la’akari da ma'anoni akan ya karanta da kansa.

Akwai lada a cikin sauraren karatun Alƙur'ani kamar yadda yake akwai a cikin karanta shi.

Falalar Abdullahi bin Mas'ud - Allah Ya yarda da shi -, inda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya so ya ji karatun daga bakinsa, wannan yana nuni akan kwaɗayin Ibnu Mas'ud - Allah Ya yarda ad shi - akan neman Alƙur'ani da haddace shi da kuma kyautata shi.

Falalar yin kuka dan tsoron Allah - Mai girma da ɗaukaka - a lokacin jin ayoyinSa, tare da lazimtar nutsuwa, da kyakkyawan yin shuru, da kuma rashin kururuwa.

التصنيفات

Ladaban Karanta Al-qur’ani da kuma Haddace shi