إعدادات العرض
Mafarki na gari daga Allah ne, mummunan mafarki kuwa daga Shaiɗan ne, idan ɗayanku ya yi mummunan mafarkin da yake jin tsoronsa to ya yi tofi a hagunsa, kuma ya nemi tsarin Allah daga sharrinsa, to cewa shi ba zai cutar da shi ba
Mafarki na gari daga Allah ne, mummunan mafarki kuwa daga Shaiɗan ne, idan ɗayanku ya yi mummunan mafarkin da yake jin tsoronsa to ya yi tofi a hagunsa, kuma ya nemi tsarin Allah daga sharrinsa, to cewa shi ba zai cutar da shi ba
Daga Abu Katadah- Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mafarki na gari daga Allah ne, mummunan mafarki kuwa daga Shaiɗan ne, idan ɗayanku ya yi mummunan mafarkin da yake jin tsoronsa to ya yi tofi a hagunsa, kuma ya nemi tsarin Allah daga sharrinsa, to cewa shi ba zai cutar da shi ba".
الترجمة
العربية বাংলা English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Tiếng Việt සිංහල ئۇيغۇرچە Kurdî Kiswahili Português தமிழ் Nederlands অসমীয়া ગુજરાતી አማርኛ پښتو ไทย മലയാളം नेपालीالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa kyakkyawan mafarki mai faranta rai a cikin mafarki to daga Allah ne, mummunan mafarki shi ne mafarkin da yake ƙi kuma yake baƙanta rai to daga Shaiɗan ne. Wanda ya ga abinda yake ƙinsa (a mafarki) to ya yi tofi a ɓangaren hagunsa, kuma ya nemi tsarin Allah daga sharrinsu; to cewa shi ba zai cutar da shi ba, inda Allah Ya sanya abinda aka ambata (na Addu’a) sababi ne na kuɓuta daga abin ƙi na abinda jeranta akan mafarki.فوائد الحديث
Kyakkyawan mafarki da mummuna wani abu ne daga abinda mai barci yake ganinsa a cikin barcinsa na abubuwa, sai dai (Kalmar: Ru'uya) ta fi rinjaye akan abinda yake ganinsa na alheri da abu mai kyau, kuma (Kalmar: Hulum) ta fi rinjaye akan abinda yake ganinsa na sharri da mummuna, kuma ana anfani da kowane ɗayan daga cikinsu a bigiren ɗayan.
Rabe-raben mafarki:
1- Kyakkyawan mafarki, shi ne mafarki na gaskiya kuma bushara daga Allah da (mutum) yake ganinsa ko agane masa.
2- Zancen zuci shi ne abinda mutum yake zantar da kansa a farke.
3- Baƙantawa da tsoratarwar Shaiɗan da razanarwa daga gare shi dan ya baƙanta ran ɗan Adam.
Abinda aka ambata a taƙaice daga Babin kyakkyawan mafarki abubuwa ne uku: Shi ne ya godewa Allah akansa, kuma ya yi albushir da shi, kuma ya faɗawa wanda yake so shi banda wanda yake ƙinsa.
Abinda aka ambata a taƙaice daga laduban mummunan mafarki abubuwa ne guda biyar:
Ya nemi tsarin Allah daga sharrinsa, da kuma sharrin Shaiɗan, kuma ya yi tofi a hagunsa sau uku lokacin da ya farka daga baccinsa, kuma kada ya faɗawa kowa shi, idan ya yi nufin komawa baccinsa to ya juya daga ɓangaren da yake akansa; to cewa shi ba zai cutar da shi ba.
التصنيفات
Ladaban Mafarki