إعدادات العرض
Haƙiƙa kin faɗi kalmar da za'a cakuɗata da ruwan kogi da ta canza shi
Haƙiƙa kin faɗi kalmar da za'a cakuɗata da ruwan kogi da ta canza shi
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ya isheka abu kaza da abu kaza daga Safiyya, - wani daga maruwaita ya ce: Tana nufin cewa ita gajera ce - sai ya ce: «Haƙiƙa kin faɗi kalmar da za'a cakuɗata da ruwan kogi da ta canza shi» ta ce: Kuma na kwaikwayi wani mutum gare shi , sai ya ce: «Bana son ace na kwaikwayi wani mutum koda kuwa (na karɓi) abu kaza da abu kaza».
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Türkçe اردو 中文 हिन्दी Tagalog Kurdî Русский Tiếng Việt অসমীয়া Nederlands Kiswahili አማርኛ සිංහලالشرح
Nana Aisha Uwar muminai A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ya isheka daga Safiyya - tana nufin Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - cewa daga cikin aibukanta na jiki ita gajera ce, sai ya ce: Haƙiƙa kin faɗi kalmar da da za'a cakuɗata da ruwan kogi da ta rinjaye shi ta canjashi ta kuma ɓata shi, ta ce: Kuma na aikata irin aikin wani mutum dan ɓata shi, sai Annabi - tsira da amincin Allsh su tabbata agare shi - ya ce: In ya faɗi aibinsa ba ya faranta mini rai, ko in kwaikwaye shi in aikata irin aikinsa ko in faɗi irin maganarsa ta fuskar tauyewa ko da kuwa an bani wani abu mai yawa na duniya akan haka.فوائد الحديث
Gargaɗarwa da kuma tsoratarwa daga yi da mutum.
Kwaikwayar yanayi da kwaikwayon mutane ta hanyar wulaƙantarwa da tauyewa yana daga yi da mutum wanda yake haramun ne.
Siffanta aibuka na jiki wani yanki ne na yi da mutum.
Alƙali ya ce: al-Mazju shi ne cakuɗawa da kuma canjawa ta hanyar cakuɗa waninsa da shi, ma'ana cewa wannan gibar da ace ta zama daga abinda za'a cakuɗa da ruwan kogi da ta canja shi daga yadda yake, duk da yawansa, to yaya kuwa da ace ayyuka ne kaɗan suka cakuɗa da shi.
Bayanin abin da yake faruwa tsakanin ma'aurata na kishi.
Rashin tabbatarwarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga wani aiki abin ƙi.
Wulaƙantar da sha'anin duniya da abinda ke cikinta idan an haɗa da yardar Allah - Maɗaukakin sarki - da kuma rashin fushinSa.
Musulunci Addini ne na ɗabi'u masu kyau, haƙiƙa an yi umarni da kiyaye mutunci kada a keta shi da magana ne ko da aiki; domin cewa shi yana daga abinda yake gadar da gaba da ƙiyayya tsakaknin musulmai.
التصنيفات
Munanan Halaye