إعدادات العرض
Ku saurara lallai cewa duniya tsinanniya ce, kuma abinda ke cikinta ma tsinanne ne, sai ambatan Allah da abinda ke jiɓintarsa da malami ko mai neman ilimi
Ku saurara lallai cewa duniya tsinanniya ce, kuma abinda ke cikinta ma tsinanne ne, sai ambatan Allah da abinda ke jiɓintarsa da malami ko mai neman ilimi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Ku saurara lallai cewa duniya tsinanniya ce, kuma abinda ke cikinta ma tsinanne ne, sai ambatan Allah da abinda ke jiɓintarsa da malami ko mai neman ilimi".
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Tiếng Việt සිංහල Kurdî தமிழ் Nederlands Kiswahili অসমীয়া ગુજરાતી Magyar ქართული Românăالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa duniya da abinda ke cikinta abin ƙine a wurin Allah abin zargi abin bari abin nisantarwa, kuma abinda ke cikinta abin bari ne ba abin yabo bane; dan kasancewarta da dukkan abinda ke cikinta yana shagaltarwa daga barin Allah, kuma yana nisantarwa daga gare shi, saidai ambatan Allah da abinda ya kusance shi ya zama yana da jinsi da shi, cikin abinda Allah Ya so shi, ko masanin ilimi na shari'a wanda yake koyar da mutane, ko mai neman ilimin shari'a ɗin.فوائد الحديث
La'antar duniya ba ta halatta kai tsaye; dan zuwan hadisan da suke hani daga hakan, saidai la'antar abinda ke nisantarwa daga Allah - Maɗaukakin sarki - a cikinta kuma yake shagaltarwa daga biyayyrSa to yana halatta.
Dukkan abinda ke cikin duniya to wasa ne kuma shagala ne sai ambatan Allah da abinda yake sababi kuma mai taimako a cikin hakan.
Bayanin falalar ilimi da ma'abotansa da kuma ɗalibansa.
Ibnu Taimiyya ya ce: Kaɗai ana zargin haramun ne bata fuskarsa ba, ko halal ta hanyar neman yawaitawa da alfahari, da abinda ake riƙa dan nufin fariya da gasa, to wannan shi ne wanda yake abin ƙi gurin masu hankali.
التصنيفات
Zargin Son Duniya