Cewa su sun ce: Ya Manzon Allah, lallai mu mun kasance muna ci ba ma ƙoshi, ya ce: «Wataƙila kuna ci ne a rarrabe?» Ya ce: Eh. Ya ce: @«To ku haɗu akan abincinku, kuma ku ambaci sunan Allah akansa, za'a sanya muku albarka a cikinsa».

Cewa su sun ce: Ya Manzon Allah, lallai mu mun kasance muna ci ba ma ƙoshi, ya ce: «Wataƙila kuna ci ne a rarrabe?» Ya ce: Eh. Ya ce: @«To ku haɗu akan abincinku, kuma ku ambaci sunan Allah akansa, za'a sanya muku albarka a cikinsa».

Daga Wahshi ɗan Harb - Allah Ya yarda da shi -: Cewa su sun ce: Ya Manzon Allah, lallai mu mun kasance muna ci ba ma ƙoshi, ya ce: «Wataƙila kuna ci ne a rarrabe?» Ya ce: Eh. Ya ce: «To ku haɗu akan abincinku, kuma ku ambaci sunan Allah akansa, za'a sanya muku albarka a cikinsa».

[Hasan ne]

الشرح

Wasu daga cikin sahabbai sun tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai suka ce: Lallai mu mun kasance muna ci amma bama ƙoshi. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce musu: Wataƙila kuna rarrabuwa a lokacin ci; sai kowa ya ci shi kaɗai? Suka ce: Eh. Ya ce: To ku haɗu ku ci ba'a rarrabe ba, kuma ku ambaci sunan Allah a lokacin ci da faɗin: Bismillah (Da sunan Allah), za'a sanya muku albarka a cikinsa, kuma zaku ƙoshi.

فوائد الحديث

Haɗuwa a abinci da kuma ambatan Allah a lokacin ci sababi ne na samun albarka a cikin abinci, da kuma ƙoshi daga cinsa.

Rabuwa dukkaninta sharri ce, haɗuwa kuwa dukkaninta alheri ce.

Kwaɗaitarwa akan haɗuwa da kuma ambatan Allah a lokacin abinci.

Sindi ya ce: Da haɗuwa ne albarkatu suke sauka a cikin abin ci, kuma da ambatan Allah ne Shaiɗan yake hanuwa daga kaiwa ga abinci.

التصنيفات

Ladaban cin Abinci da Shan Abun Sha