Ku yi kirdadon daren Lailatul-ƙadri a cikin mara daga goman ƙarshe na Ramadan

Ku yi kirdadon daren Lailatul-ƙadri a cikin mara daga goman ƙarshe na Ramadan

Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku yi kirdadon daren Lailatul-ƙadri a cikin mara daga goman ƙarshe na Ramadan".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar akan yin ƙoƙari a nema da kirdadon daren lailatul-ƙadr da yawaita aiki na gari, shi ne mafi ƙauna ya kasance a darare na mara daga goman ƙarshe a Ramadan a kowace shekara, sune: Ashirin da ɗaya, da ashirin da uku, da ashirin da biyar, da ashirin da bakwai, da ashirin da tara.

فوائد الحديث

Falalar lailatul-ƙadr da kwaɗaitarwa akan kirdadonsa.

Daga hikimar Allah da rahamarSa cewa Ya ɓoye wannan daren dan mutane su yi ƙoƙari a cikin ibada, dan neman sa, sai ladansu ya yi yawa.

Daren Lailatul-ƙadr a goman ƙarshe na Ramadan (yake), kuma an fi ƙauna a mara daga gare shi .

Daren Lailatul-ƙadr ɗaya ne daga dararen goman ƙarshe na Ramadan, shi ne daren da Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya saukar da Al-Kur'ani a cikinsa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma Ya sanya wannan daren ya fi wata dubu a albarkarsu, da girman darajarsu, da tasirin aiki na gari a cikinsu.

An ambaci (Lailatul-ƙadr) da yi wa (Dal ) ɗauri da hakan, kodai daga ɗaukaka ne, sai ace: Wane mai girman daraja ne, sai raɓawar daren ta zama daga babin raɓawar abu zuwa siffarsa, wato dare maɗaukaki, yana nufin cewa shi mai girman daraja ne da ɗaukaka da buwaya da matsayi zuwa ƙarshensa, (lallai Mu Mun saukar da shi a cikin wani dare Mai albarka).

[al-Dukhan: 3],

ko kuma daga ƙaddarawa ne: Sai raɓawar gare shi ta zama daga raɓawar Zarfi zuwa abinda yake tattaroshi, wato wannan daren wanda a cikinsa akwai ƙaddarawar abinda yake gudana a cikin shekara, (A cikinta ne ake rarraba kowane al'amarin da ake hukuntawa)

[al-Dukhan: 4].

التصنيفات

Goman Qarshe na Watan Azumi